Jiya Laraba, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasa Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Zambiya Mulambo Haimbe a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A yayin ganawarsu, Wang Yi ya yi bayani game da ra’ayoyin cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20. Ya ce, kasar Sin tana fatan kara yin mu’amala da kasar Zambiya game da fasahohin gudanar da harkokin cikin gida, tana kuma goyon bayan kasar Zambiya wajen neman hanyar bunkasuwa da ta dace da halin da kasar take ciki, kuma za ta ba da taimako ga kasar Zambiya kan ayyukan zamanintar da kasa. A watan Satumba na bana, za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing. Kasar Sin na fatan yin amfani da wannan muhimmiyar dama wajen zurfafa zamuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka, gami da inganta aikin gina makomar Sin da Afirka ta bai daya zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare kuma, Mista Haimbe ya ce, kasar Zambiya tana fatan karfafa dangantakar hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi, a wannan lokaci da huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ta cika shekaru 60. (Mai Fassara: Maryam Yang)