A yau Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron dandali ministoci karo na 7, na tattauna matakan karfafa cudanya, da samar da karfin gwiwa tsakanin sassan Asiya ko CICA a takaice.
Yayin da yake halartar taron ta kafar bidiyo, Wang Yi ya ce, sauye-sauye na tsawon karni na ci gaba da gudana cikin sauri, kuma duniya ta shiga wani sabon lokaci na tangal-tangal da canji. Kuma cimma yanayin tsaro, da ingiza ci gaba, da samar da hadin gwiwa, da neman cimma moriya tare, sun zama muradun gaggawa na mafi akasarin kasashen duniya.
- Xi Jinping: Ana Kokarin Raya Tsibirin Hainan Bisa Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin
- Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Cimma Sabbin Nasarori A Fannin Zamanantarwa Yayin Da Ake Bikin Cikar Qiao Shi Shekaru 100 Da Haihuwa
Game da hakan, dandalin CICA na iya taka rawar gani ta musamman, a fannin gina al’ummar Asiya mai makomar bai daya, da bude sabon babin bunkasa nahiyar bai daya. Ya ce, da farko akwai bukatar nacewa zaman jituwa tare, da wanzar da tsaro na bai daya. Kana a hada hannu wajen aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” don yayata walwala da ci gaba. Kana na uku, a martaba mabambantan wayewar kai, da ingiza musaya da koyi da juna. Kana na 4, a aiwatar da tsarin cudanyar dukkanin sassa, da gina kyawawan yankuna.
Kaza lika, Wang Yi ya jaddada cewa, salon zamanantarwa na Sin yana bin turba ce ta samar da ci gaba cikin lumana, da samar da karin damammaki ga kasashen Asiya. A daya bangaren kuma, Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashe mambobin dandalin na CICA, wajen bibiyar asalin muradun da aka sanya gaba, da nacewa dunkulewa, da sahihin tsarin gudanarwa, da hada karfi wajen samar da sabon salon wayewar kai don cimma nasarar ci gaba na bai daya. (Saminu Alhassan)