Yau Jumma’a, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da ’yan jaridu bayan taron ministoci na hadin gwiwa na Lancang-Mekong karo na 10, inda ya bayyana matsayin kasar Sin kan wasu batutuwan tarihi.
Wang Yi ya ce, yau rana ce ta musamman ga kasar Sin, domin a wannan rana a shekarar 1945, kasar Japan ta sanar da ba da kai ba tare da wani sharadi ba cikin yakin da ta kaddamar kan kasar Sin, tare da sa hannu kan sanarwar Potsdam. Yakin da kasar Japan ta tayar ya haddasa babbar illa ga al’ummomin kasar Sin da na kasashen nahiyar Asiya, har ma ga al’ummomin ita kanta kasar Japan din. Amma, har zuwa yanzu, wasu ’yan siyasan kasar Japan suna neman musanta gaskiyar batun, da yunkurin gyara tarihi. Lamarin da ya bata ran al’ummomin kasa da kasa, da keta kundin tsarin MDD. Ya ce ya kamata a mutunta ainihin tarihi, ta yadda za a samu girmamawa. Ya kamata a koyi darasi daga tarihi, ta yadda za a nemi sabon ci gaba. Kana, ya kamata a tuna da tarihi, domin magance sake aikata kuskure. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp