A yau Lahadi, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da mukadashin ministan wajen Iran Karim Bagheri.
Yayin zantawar ta su, Wang Yi ya bayyana cewa, bangaren Sin ya dade yana kan matsayin adalci a harkokin yankin Gabas ta Tsakiya, yana goyon bayan bangarori daban daban su kiyaye moriyarsu, musamman ma goyon bayan dawo da hakkin al’ummar Falasdinu.
- Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Lambar Zinare A Gasar Kwallon Tebur Ta Kungiyoyin Mata A Gasar Olympics Ta Paris
- A Tsinke Sarkar Rashin Adalci A Nijeriya Nakuda
Kaza lika, bangaren Sin yana adawa, da kuma sukar kisan mutane a boye, yana kallon hakan a matsayin matukar keta ka’idojin dangantakar kasa da kasa, da keta hurumin tsaron ikon mulkin kasa da mutuncin kasar Iran, kuma hakan ya gurgunta ci gaban tattaunawar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da illata zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
Har ila yau, bangaren Sin na goyon bayan bangaren Iran a fannin kiyaye tsaron ikon mulkin kasa, da mutuncin al’ummarta, yana goyon bayan bangaren Iran a kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kana yana fatan bunkasa mu’ammalar kut da kut da bangaren Iran.
A nasa bangare, Bagheri ya jinjinawa matsayin Sin na tsayawa adalci kan batun ricikin Falasdinu da Isra’ila, yana mai fatan Sin din za ta ba da karin gudummawa ga saukaka halin da ake ciki, da kuma inganta tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya. (Safiyah Ma)