• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Kasashen Turai Da Rasha

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Kasashen Turai Da Rasha
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar 22 ga wata, Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin kolin ya bayyana cewa, yadda kokarin kasar Sin na zamanintar da kanta zai amfani kasar da ma duniya baki daya.

Sin ta riga ta cimma gagarumar nasara wajen dakile da kandagarkin cutar COVID-19, ana farfado da tattalin arziki da zamantakewar al’ummarta, lamarin da ya sa kasar Sin za ta ci gaba da zama muhimmin injin na sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Bisa dimbin hakikanan abubuwa, kasar Sin ta shaida cewa, neman ci gaba cikin lumana ba kawai wata hanya ce mai yiyuwa ba,amma wata hanya ce mai dacewa sosai. Sin za ta ci gaba da bin hanyar, tare da fatan yin kokari tare da sauran kasahe wajen bin hanyar neman ci gaba cikin lumana.

  • Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dage Zaben Sanatan Enugu Ta Gabas

Wang Yi ya yi wannan furuci ne a gaban wakilan kafofin watsa labarai, bayan da ya kammala ziyararsa a kasashen Faransa, Italiya, Hungary da Rasha, da kuma halartar taron tsaro na Munich karo na 59.

Kasar Amurka tana ta kara gishiri kan batun balan-balan maras matuki na kasar Sin da ya shiga sararin saman Amurka bisa kuskure, don haka kasashen duniya sun mai da hankali sosai kan kwarya-kwaryar ganawa a tsakanin bangarorin biyu a yayin taron tsaron Munich. Game da batun, Wang Yi ya nuna cewa, yayin da yake ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya kalubalanci Amurka da ta dakatar da yin wannan abun wauta don biyan bukatunta a siyasance.

Ya kamata Amurka ta yi kokari da sahihiyar zuciya wajen warware matsalar da za ta kai ga lalata dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu sakamakon wannan batu. Amma idan Amurka na son kara tsananta wannan batu, tabbas kasar Sin za ta ci gaba da mayar da martani har zuwa karshe. (Kande Gao)

Labarai Masu Nasaba

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Matsalar Tsaro Ta Haifar Da Koma-baya A Jihohin Arewa  —Masari

Next Post

Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Neman A Sauke Babban Sufeton ‘Yansanda

Related

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

5 hours ago
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata
Daga Birnin Sin

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

6 hours ago
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

8 hours ago
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya
Daga Birnin Sin

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

9 hours ago
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

16 hours ago
Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

18 hours ago
Next Post
Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Neman A Sauke Babban Sufeton ‘Yansanda

Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Neman A Sauke Babban Sufeton ‘Yansanda

LABARAI MASU NASABA

UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.