Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yiwa manema labarai karin haske, game da ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Saudiyya, tare da halartar taron kolin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko, da taron kolin kasar Sin da hukumar hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf GCC.
Wang Yi ya ce ziyarar da shugaba Xi ya yi a gabas ta tsakiya tsakanin ranakun Laraba zuwa Asabar, ta bude sabon babi na zurfafa ci gaban alakar Sin da Saudiyya, da sauran kasashe mambonin GCC daga dukkanin fannoni.
Ya ce yayin da yake masarautar Saudiyya, baya ga halartar taron kolin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko, da taron kolin kasar Sin da hukumar hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf GCC, da ziyarar aiki a kasar Saudiyya, shugaba Xi ya kuma gana kai tsaye da shugabannin kasashen larabawa kusan 20, wanda hakan ya sanya ziyarar ta sa ta wanan karo, zama mafi muhimmanci ta fuskar ayyukan diflomasiyya Sin da kasashen Labaraba, tun bayan kafuwar janhuriyar jamaar kasar Sin.
Wang Yi ya kuma bayyana wannan muhimmiyar ziyara da shugaba Xi ya yi, a matsayin babban jigon karfafa diflomasiyya, wanda ya nuna kyakkyawan zabin da Sin tare da kasashen larabawa suka yi a fannin karfafa goyon baya, da tsare tsaren ayyuka, a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubale. (Saminu Alhassan)