Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira da a gaggauta kama hanyar ci gaba ba tare da gurbata muhalli a yankin tsaunin Himalaya, domin ingiza samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin.
Wang Yi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin taro karo na 3 na kasashen yankin tsaunin Himalaya domin hadin gwiwa, wanda ya gudana a Nyingchi, dake jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kudu maso yammacin kasar Sin.
- Tirka-tirkan Takardun Tinubu: Ku Zo Mu Hada Hannu Don Fafutukar Wanzar Da Gaskiya – Atiku Ya Roki Obi, Kwankwaso
- Tsige McCarthy Daga Mukaminsa Ya Nuna Me Ake Nufi Da “Dimokradiyyar Amurka”
A cewarsa, shimfidar kasa ta hade kasashen dake yankin, inda suke da al’adu iri daya har ma da makoma, haka kuma suna da ra’ayi iri daya kan kare muhalli, baya ga kasancewarsu abokan hulda a fannin zamantar da kansu.
Wang Yi ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da wadannan kasashe wajen yayata damarmakin samun ci gaba da gina al’umma mai makoma ta bai daya tare da su, da bayar da gudunmuwa ga samar da wadata da kwanciyar hankali da kare muhallin yankin da ma na duniya.
Yayin taron an fitar da Shawarar Nyingchi, wadda ke da nufin zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa a yankin tsaunin Himalaya. (Fa’iza Mustapha)