Wani mummunan lamari ya afku a unguwar Tudu da ke Maiduguri a lokacin da akaji karar harbe-harben bindiga da dama wanda ya firgita sannan ya tilastawa mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu, a tunaninsu Boko Haram ce ta kawo hare-hare.
Sai dai kuma, a wani yanayi mai ban mamaki, harbin bindigar ya fito ne daga bindigar AK-47 na sajan Ɗansanda, wanda ya harbe mahaifin nasa.
- An Yi Asara Kimanin Naira Biliyan 500 Sakamakon Zanga-zanga – Minista
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Sojoji Sun Ƙona Motocin Sintiri 2 A Sakkwato
Talla
Ɗansandan mai suna Linus Wadzani da ke aiki da Mopol 6, ya bude wa mahaifinsa wuta mai suna ASP Wadzani Ntasiri mai shekaru 70 (mai ritaya) a cikin gidansu.
Nan take aka tsare wanda ake zargin a hedikwatar ‘yansandan Maiduguri.
Talla