A karo na biyu a bana, wani Alhajin Nijeriya daga karamar hukumar Gumi ta Jihar Zamfara, ya tsinci makudan kudaden Turai wato Euro har €1,75 0, kwatankwacin Nairar Nijeriya Miliyan N2,876,475 a Harami wato Masallacin Ka’aba.
Alhajin mai suna, Muhammad Na-Allah, ya mika wadannan makudan kudade ne ga hannun Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriyar, Malam Jalal Arabi, domin neman mai su.
- Kamfanin Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin Ya Shiga Kasuwar Kenya
- Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG
Da yake karbar kudaden, shugaban Hukumar Alhazan ta Nijeriya, Malam Jalal Arabi ya fassara aikin alhairin da Alhajin ya yi da sunansa wato Na-Allah.
Malam Jalal Arabi wanda ya ce aikin Alhaji Na-Allah ya nuna cewar akwai alamun tarbiyar da aikin hajji ke koyarwa ta shigi Alhaji Na-Allah, a tarbiyance da dabi’ance.
Indan za a iya tunawa, a makon da ya gaba ma an samu wani Alhaji daga Jihar Jigawa da shima ya tsinci kudaden kasar Ingila, da na Kasar Rasha da Riyal din Saudi Arabia.