A wani yunƙuri na inganta kula da kiwon lafiya, wani asibitin ƙwararru mai zaman kansa da ake kira ‘Best Choice’ ya ɗauki gaɓarar kula da kiwon lafiyar jarirai tare da ƙaddamar da sashin fasaha don kula da Lafiyar Jarirai da aka tsara don magance ciwon shawara da hana lalacewar kwakwalwar ga jarirai.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Shugaban Asibitin, Auwal Muhammad Lawal, ya ce na’urar ita ce irinta ta farko wanda kwararrun likitoci ke amfani da ita wajan juyen jini cikin fasaha don inganta sakamakon jiyya ga yara.
- Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Miyagun Kwayoyi A Kano
- Tinubu Ya Sake Nada Farfesa Sheshe Shugaban Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano
A nasa ɓangaren, Dr Abdulmalik Saminu, ya bayyana cewa na’ura ce mai cike da fasaha da ke ɗaukar nauyin fitowar haske kaso 70% na ban mamaki da ke daidaita buƙatar ƙari ko juyen jini.
Ya ƙara da cewa ɓullo da wannan na’ura ta zamani ya nuna wani gagarumin ci gaba ne da Asibitin ‘Best Choice’ ya bullo da shi don kula da kiwon lafiyar jarirai.
Saminu ya ce Sashin Kula da Lafiyar Jarirai na iya yin maganin ciwon shawara yadda yakamata cikin ƙwarewa ba tare da ɗaukar yin doguwar jinya ga iyalai ba, da kuma sauƙin kashe kuɗaɗe.
“Mun fahimci irin yadda iyaye ke faman shan wahala game da yanayin lafiyar ƙananan yara”
“Saboda haka ne muka mai da hankali kan wannan fasaha don sauƙaƙe nauyin da ke kan iyalai da kuma samar wa yara yanayi mafi kyawu, domin samun rayuwa mai kyau”. In Ji Auwal.
Shugaban Asibitin ya bayyana cewa na’urar ita ce irin ta ta farko a Arewacin Nijeriya, kuma ta uku a fadin Nijeriya, kuma tana ba da cikakkiyar kariya da maganin jiyya ga jarirai.
Dr. Abdulmalik Saminu, babban kwararre likita ne a fannin kiwon lafiya ya bayyana fatansa cewa wannan ci gaban zai ƙara ƙarfafa matsayin asibitin na ‘Best Choice’ a matsayin jagora a fannin kula da kiwon lafiyar ƙananan yara, tare da bai wa iyalai ƙwarin guiwa kan kula da ‘yan uwansu.
Saminu ya godewa mamallakin asibitin bisa namijin ƙoƙarin da ya yi na samar da wannan fasaha ta zamani duk da irin tsadar da take da shi.
Da wannan na’urar ta Kula da Lafiyar Jarirai, iyalai da ‘yan uwa ba sa buƙatar neman tafiya ƙasashen waje don neman magani, kamar yadda asibitin na ‘Best Choice’ ke bayar da tabbas kan haka wajen bayar da kulawa ta musamman a cikin gida.