Wani dan Nijeriya mai suna, Obinna Igbokwe, a ranar Alhamis ya harbe matarsa Tangela da kakarsa kafin ya kashe kansa a jihar Texas ta Amurka.
Ko da yake matar ta samu munanan raunuka kuma tana kwance a asibiti, kakar ta rasu sakamakon raunin da ta samu.
- Matar Da Ake Yi Wa Allurar Tazarar Haihuwa Ta Haifi ‘Yan Hudu Rigis
- Fashewar Tukunyar Gas Ta Raunata Mutan 20 Da Kona Wasu Shaguna A Kano
A cewar wani rahoto na kasar, Igbokwe ya bar gida ne tare da dansa dan watanni uku, bayan ya harbe matan biyu a ka a ranar Laraba.
Yayin da suka gudu, Igbokwe ya ajiye yaron a kujerar mota a wani otal.
Lokacin da aka sanar da ‘yan sanda cewar yana yankin, wanda ake zargin ya harbe kansa ya mutu sakamakon raunin da ya samu.
Wata sanarwa da ofishin Sheriff ta fitar a ranar Alhamis ta ce, “A ranar 2 ga watan Yuni, 2022, da misalin karfe 12:00 na safe, jami’an tsaro na ofishin Sheriff na Montgomery sun tuntubi jami’an ‘yan sanda na Corsicana kuma suka ba da shawarar cewa Mansa Igbokwe ke kula da su.
“A cewar hukumar ‘yan sanda ta Corsicana, wani namiji ya ajiye yaron a kujerar mota a wani otal da ke yankin ya ce zai dawo nan da nan, amma bai dawo ba.
“Tunda namijin bai dawo ba, sai aka tuntubi hukumar ‘yan sanda ta Corsicana, inda suka samu labarin ya bar mutumin a cikin wata farar motar fasinja, wadda suka yi imanin Igbokwe ne.
“An aika da ƙarin bayanai ga jami’an tsaro na yankin Ellis da Navarro suna sanar da su cewa Igbokwe na yankin.
“Da misalin karfe 1:05 na dare jami’an hukumar ‘yan sanda ta Ennis sun gano wata farar mota kirar Honda Igbokwe tana tuki kuma suka yi yunkurin tsayar da motar.
“Bayan sun bibiyi motar kirar Honda sai ta tsaya a wani wurin ajiye motoci inda jami’ansu suka lura kuma suka ji karar harbin bindiga daya fito daga cikin motar Honda.
“Jami’an tsaro sun fara daukar matakan ceton rai tare da kiran jami’an lafiya, amma saboda tsananin raunin da Igbokwe ya samu abun ya ci tura, an garzaya da shi wani asibiti mai suna Dallas da misalin karfe 5:20 na safe.
“Mansa Igbokwe yana cikin koshin lafiya kuma bai samu matsala ba kuma ya sake haduwa da iyalinsa. Zuciyarmu tana tare da dangin da wannan mummunan laifi ya shafa kuma muna aiki tare da wadanda abin ya shafa don ganin sun sami tallafi da taimako.”