Wasu Rahotanni sun bayyana cewa an rasa wani Jariri dan kwana ɗaya da haihuwa a duniya a asibitin waziri gidado dake nan Kano.
An wallafa wannan labarin a shafin sada zumunta na Arewa Radio da ke Kano, inda suka bayyana cewa bayan mahaifiyar yaron ta haihu a gida a ranar Alhamis sai ta kamu da rashin lafiya, inda aka garzaya da ita asibitin domin kula da lafiyarta.
- Gwamna Abba Kabir Yusuf: Kano Na Bukatar Sabuwar Alkibla
- Tinubu Ya Gana Da Ganduje Da Shugabannin APC Na Kano A Villa
Da misalin karfe 8 na dare tana cikin halin rashin lafiya wata mata ta dinga hilatar kakar yaron har ta tafi da jaririn nasu wanda kawo yanzu babu labarinsa.
Mahaifin yaron mai suna Aliyu ya ce, ya tafi sallah ya bar mahifiyar yaron da kakar yaron a asibiti sai dawo wa ya yi ake gaya masa yaron ya bata.