Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa wani soja da ke bakin aiki ya mutu bayan wani mutum mai taɓin ƙwaƙwalwa ya kai masa hari a yankin Imota da ke Ikorodu, Jihar Legas.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 16 ga Nuwamba, 2025, da misalin karfe 4 na yamma lokacin da aka tura sojan don ayyukan tsaro na cikin gida.
- PDP Ta Ɗage Taronta Bayan Arangamar ‘Yansanda Da ‘Yan Daba A Abuja
- Zaɓen 2027: Malami Zai Fito Takarar Gwamna A Kebbi
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojan Kasa, Rundunar Soja ta 81, Musa Yahaya, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce, sojan yana kokarin kwantar da wani ɗan rikici ne lokacin da maharin ya buga masa wani babban katako a kai, wanda ya yi sanadiyyar ji masa mummunan rauni.
Sauran sojojin da suke aiki tare, sun shawo kan lamarin cikin gaggawa, inda suka harbe maharin sannan suka ƙwato bindigar sojan da maharin ya ɗauka.
Yahaya ya kuma bayyana cewa, an garzaya da sojan da ya ji rauni zuwa Babban Asibitin Ikorodu, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Rundunar ta ce, daga baya an binne sojan da ya mutu bisa yadda Musulunci ya tanada, inda Mukaddashin Kwamandan Rundunar da sauran jami’an rundunar suka halarta.














