Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai suna Abdullahi Isiyaku mai shekaru 37 a duniya, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da APC a karamar hukumar Maigatari.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa Leadership Hausa.
- Ya Kamata Amurka Ta Maida Martani Game Da Shakkun Da Ake Mata Dangane Da Fashewar Bututun Nord Stream
- Tabbas Jami’an Tsaro Za Su Kare Jami’an Zabe Babu Haufi – Farfesa Yakubu
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da jam’iyyar adawa ta PDP ke gudanar da wani taro a Maigatari.
Shiisu ya bayyana cewa rikicin ya barke ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar PDP suka isa sakatariyar jam’iyyar APC da ke Gangare, inda suka kai wa wani Abdullahi Isiyaku hari.
Ya ce an garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da shi zuwa Babban Asibitin Gumel, inda daga baya daya ya mutu a lokacin da yake jinya.
Shiisu, ya ce an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a rikicin.
Ya ce an mika lamarin zuwa ga sashen binciken manyan laifuka (SCID) don yin bincike mai zurfi.