• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wannan Abu Ya Sa Afirka Ta Zama Abin Koyi

by CMG Hausa
3 years ago
Afirka

Yau 18 ga watan Yuli rana ce da MDD ta kebe don tunawa da Nelson Mandela.

Idan an ba ni damar takaita ruhin marigayi Mandela da kalma daya, zan zabi “Hakuri”. Saboda ya taba bayyana cewa, “Lalata abu na da sauki, amma wanda ya dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya shi ne jarumi.”

  • Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-3 Na Kasar Sin Ya Rabu Da Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

A sabili da ruhinsa na hakuri, bayan da Mandela ya kammala zamansa na shekaru 28 a gidan kurkuku, kuma ya zama shugaban kasa bakar fata na farko a tarihin kasar Afirka ta Kudu, bai nemi yin ramuwar gayya ga mutanen da suka taba cin zarafinsa ba.

Don neman ganin an kafa wata sabuwar kasa, da samun sulhu tsakanin kabilu daban daban na kasar, ya nuna hakuri ga ‘yan kasarsa fararen fata, ta yadda a karshe dai ya cimma burin kare hakkin bakaken fata da kuma tabbatar da zaman daidaito a tsakaninsu da fararen fata.

A sauran kasashen Afirka ma, muna iya ganin yadda ra’ayi na hakuri ke taka muhimmiyar rawa. Misali a kasar Rwanda. Bayan abkuwar kisan kiyashi a shekarar 1994, wanda ya haddasa mutuwar mutane miliyan 1 a kasar, ba a ga wata ramuwar gayya daga ‘yan kabilar Tutsi ba. Maimakon haka, abun da aka yi shi ne neman samun maslaha. Cikin ‘yan kabilar Hutu dubu 120 da suka sa hannun kisan kiyashin, ban da yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 90 da suka fi taka rawar aikata laifukan, sauran sun samu damar gyara halinsu. Hakurin da aka nuna ya tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan al’umma, inda wannan yanayi ya sa kasar kiyaye saurin karuwar tattalin arzinta na kashi 70% ko fiye da haka, tun bayan shekarar 2003.

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Abin takaici shi ne, ra’ayi na hakuri da marigayi Mandela da sauran ‘yan Afirka ke da shi, har yanzu bai yi tasiri a wasu wurare ba, musamman ma babbar kasar da take daukar kanta a matsayin mai kare dimokuradiya da hakkin dan Adam.

A wannan kasa ra’ayin bambancin launin fata ya zama ruwa dare, inda yiwuwar ‘yan sanda su kama bakar fata ta ninka ta farar fata har sau 6. Kana an taba ganin yadda wani dan sanda ya danne wuyan wani saurayi bakar fata da gwiwa, har ya kashe shi, da yadda ‘yan sanda suka bindige wani bakar fata da ba shi da makami, wanda har aka samu raunukan bindigogi 60 a jikinsa, al’amuran da suka sanya al’ummar duniya cikin kaduwa.
Wannan kasa, ko da yake tana da karfi sosai a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, amma tana ci gaba da fama da yanayi na koma baya, ta fuskar zaman daidaito a tsakanin al’umma, da kare hakkin dan Adam.

Yadda ake nuna rashin adalci a kasar, shi ma ya sa ta yi kokarin daukar matakai na son kai a duniya, ba tare da lura da bukatun sauran kasashe ba. Abubuwan da ya kamata wannan kasa ta koya daga kasashen Afirka, suna da yawa. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Next Post
Gwamnan Oyo Ya Maye Gurbin Mataimakinsa Da Lawal Bayan Tsige shi

Gwamnan Oyo Ya Maye Gurbin Mataimakinsa Da Lawal Bayan Tsige shi

LABARAI MASU NASABA

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.