Errachidia wani gari ne dake gabashin kasar Morocco, wanda ya kasance cikin hamadar Sahara. Mazauna garin kowanensu ya san “likitocin kasar Sin”, domin wata tawagar likitocin kasar Sin ta riga ta kwashe shekaru 38 tana samar da hidimomi a can. Ana ma iya cewa kusan rabin yaran wurin likitocin Sin ne suka karbi haihuwar su, kana a kan samu iyalin da mambobinsa na zuriyoyi 3 suka taba samun taimako daga likitocin.
Kasancewar garin Errachidia wani kebabben wurin dake cikin hamada, ya sa shi rashin kayayyaki da abubuwa iri-iri, musamman ma likitoci. Saboda haka, likitoci 10 na wannan tawagar agajin aikin jinya ta Sin su kan gudanar da ayyukan tiyata fiye da 2000 a duk shekara. Wani lokaci ma, wani likita daya dake cikinsu na bukatar yin tiyata kan majiyyata 8 daya bayan daya a dare daya.
Don haka su kan yi fama da rashin barci da gajiyar aiki. Jiang Quanming, mai shekaru 56 da haihuwa, shugaba ne na wannan tawagar likitocin Sin, wanda ya taba fita hayyacinsa yayin da yake aiki sakamakon matukar gajiya. Amma duk da haka, ya tsawaita wa’adin aikinsa a wurin bisa son ransa. A cewarsa, makiyayan wurin su kan yi kokarin jure ciwon jiki yayin da suke rashin lafiya, sakamakon tsananin talaucin da suke fama da shi, abin da ya sa su cikin wani yanayi mai hadari bayan da aka kai su asibiti a karshe. Saboda haka, duk wani aikin tiyata da shi da abokan aikinsa suka yi, zai ceci ran mutum daya.
Maganar Jiang ta nuna yadda likitan yake da kishi da kokarin sadaukarwa, sai dai ba zai samu damar cimma burinsa na taimakawa mutanen garin Errachidia, in ba domin goyon bayan da gwamnatin kasar Sin ta nuna masa, da kudin da ta zuba ba. Hakika tura tawagogin agajin aikin likitanci zuwa ketare wani muhimmin bangare ne na aikin kasar Sin, na tallafawa sauran kasashen da suke da bukata.
A shekarar 1963, kasar Sin ta tura tawagarta ta farko ta ba da agajin aikin jinya zuwa kasar Aljeriya. Daga baya, cikin shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin ta tura likitoci dubu 30 zuwa kasashe da yankuna 76. Bayan da annobar Ebola ta barke a yammacin Afirka, kasar Sin ta tura likitoci fiye da 1200 zuwa wuraren da aka fi jin radadin annobar don ba da taimako. Kana a lokacin da ake samun bazuwar cutar COVID-19 a duniya, tawagogin likitocin Sin 46 dake kasashen Afirka daban daban, sun samar da gudunmowa a kokarin dakile annobar a wuraren da suke. Sa’an nan, tawagogin likitocin Sin sun ba da kyautar dimbin magunguna da sauran kayayyakin aikin jinya ga wasu asibitocin kasashe masu tasowa, gami da taimaka musu horar da masu aikin likitanci.
Ko me ya sa kasar Sin ke son ba da taimako ga sauran kasashe a fannin aikin likitanci? Dalilin shi ne aikin ya dace da al’adun Sinawa na daukaka zaman lafiya da darajanta rayukan mutane. Wannan al’adu sun sa kasar Sin son tabbatar da kwanciyar hankali maimakon ta da rikici, da kai dauki ga wadanda ke da bukata, maimakon nade hannu a yi kallo a gefe. Saboda haka, a lokacin da ake bukatar likitoci da magunguna a wasu kasashe masu tasowa, kasar Sin ta kan tura likitoci da samar da tallafi ba tare da jinkiri ba. Kana bayan da aka samu barkewar rikici a wasu kasashe, sojojin Sin su kan aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya a can, bisa izinin da Majilissar Dinkin Duniya (UN) ta ba su. Kana duk lokacin da wani iftila’i ya abku, kasar Sin ta kan tura tawagogin ceto, da aikewa da kayayyakin da ake bukata nan take, ba tare da wani jinkiri ba ko kadan.
Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafawa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa wata al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya”. A cikin gidan kasar, an samu kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun zaman jituwar al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke fuskantar, da kafa wata duniya mai jituwa.
A lokacin da ka ga yadda likitoci Sinawa suke kokarin haye wahalhalun da suke ba da taimako ga jama’a a cikin hamadar Sahara, to, za ka fahimci cewa, Sinawa na kokarin aiwatar da akidarsu ta kafa wata al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, kana burinsu na samun wata duniya mai kyau zai cika. (Bello Wang)