Abokaina, ko kun taba jin sunan “Farfajiyar kimiyya ta Sin da Afirka”? Wannan farfajiyar tana gundumar Quzhou ta lardin Hebei, kuma daya ce daga cikin cibiyoyin da kasar Sin ta gina, musamman ma domin taimakawa kasashen Afirka horar da kwararru a fannin aikin gona.
Sanin kowa ne, ba za a iya raba binciken sabbin fasahohin aikin gona da gwaje-gwajen da ake gudanar da su cikin gonaki ba. Saboda haka, jami’o’i da cibiyoyin nazarin fasahar noma na kasar Sin sun kafa “farfajiyoyin kimiyyar aikin gona” da yawa a kauyukan kasar. Na taba ziyartar daya daga cikinsu dake karkarar birnin Beijing, inda ake samun wasu dalibai fiye da 10 na jami’ar koyon fasahar aikin gona ta kasar Sin, wadanda suke kula da gonaki eka 300, inda suke noman sabbin nau’o’in ’ya’yan marmari, bisa amfani da fasahohin zamani na zuba ruwa bisa bukatar amfanin gona, da sarrafawa daga wani wuri mai nisa, da na’urorin aikin noma masu sarrafa kansu, da dai sauransu.
Bayan sun gwada da inganta fasahohin, sai a yada su zuwa wurare daban daban na kasar Sin. Dalilin da ya sa kasar Sin ke iya ciyar da al’ummun kasar, da yawansu ya kusan kaiwa kashi 20% na daukacin al’ummar duniya, bisa gonakinta, wanda fadinsu bai wuce kashi 9% na daukacin gonakin duniyarmu ba, shi ne domin wannan tsarin da kasar ke bi, na kokarin nazarin sabbin fasahohin aikin gona, tare da yada su a kai a kai.
A nata bangare, “farfajiyar kimiyya ta Sin da Afirka”, wadda aka kafa wa dalibai ‘yan kasashen Afirka, za ta kai wannan nagartaccen tsari na kasar Sin nahiyar Afirka. Tun da aka kafa farfajiyar a shekarar 2019, ta riga ta taimaka wajen horar da dalibai masu koyon fasahohin noma fiye da 60, wadanda suka zo daga kasashe 12 dake nahiyar Afirka.
Ban da haka, a shekarar 2022, kasar Sin ta kafa wani “kauyen da ake gwada fasahohin raya aikin gona da rage talauci” a kasar Malawi, inda daliban da suka samu horo a “farfajiyar kimiyya ta Sin da Afirka” suke gwadawa da nuna sabbin fasahohin noma, da taimakawa manoman wurin kyautata dabarar samar da karin amfanin gona.
Ta shirin nan na “farfajiyar kimiyya ta Sin da Afirka”, za mu iya ganin wasu hallayyan musamman na hadin gwiwar Afirka da Sin.
Da farko, ana gudanar da hadin gwiwarsu ne don biyan bukatun kasashen Afirka na daidaita wasu matsalolin da suke fuskanta. Misali, David Mutendango, wani dalibi dan kasar Zambia, ya ce a kasarsa ta Zambia, ana iya samun masara ton 1 zuwa 3 bisa gona ta kadada 1, amma yawan masarar da ake iya girba daga gonar kadada 1 ta kasar Sin ya wuce ton 6. Ganin haka ya sa shi halartar shirin “farfajiyar kimiyya ta Sin da Afirka”, don koyon fasahar samar da karin amfanin gona.
Na biyu shi ne, ana dora muhimmanci sosai kan neman samun ci gaba, yayin da ake gudanar da hadin kai tsakanin bangarorin Afirka da Sin. Noma tushen arziki. Yadda kasar Sin take taimakawa kasashen Afirka horar da kwararru masu fasahar aikin gona, da raya fasahohin zamani na noma, da samar da karin amfanin gona, ya aza harsashi domin ci gaban kasashen Afirka cikin matukar sauri a nan gaba. Kana kasar Sin na son raba fasahohin ta tare da kawayenta dake nahiyar Afirka, musamman ma a fannonin raya tattalin arziki, da rage talauci.
Abun da kasar Sin ke yi wa kasashen Afirka ya shaida sahihancinta. Sai dai me ya sa take da wannan sahihanci? Shi ne domin babbar akidar kasar ta kafa “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya”. A ganin Sinawa, dalilin da ya sa ake yawan samun rikici da tashin hankali a duniya, shi ne domin rashin daidaito tsakanin kasashe da al’ummun duniya. Idan aka bar wasu kasashe da yankuna cikin yanayi na fama da koma bayan tattalin arziki, da barin wasu mutane su ci gaba da fuskantar tamowa da talauci, to, da kyar a tabbatarwa duniyarmu da wata makoma mai haske. Wannan ra’ayi ya sa kasar Sin ke kokarin neman tabbatar da moriyar juna, yayin da take hadin gwiwa da kasashen Afirka. Kana kasar na son ganin kasashen Afirka samun hakikanin ci gaba, ta yadda za su hada gwiwarsu don kafa wata duniya mai adalci tare. Wannan buri shi ne tushen alakar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka. (Bello Wang)