Sauyawar yanayin duniya na samar da mummunan tasiri kan muhallin halittu, da tattalin arziki, gami da zaman al’umma a nahiyar Afirka.
An ce a bana akwai mutane ‘yan Afirka kimanin miliyan 1.8 da fari ya tilasta musu bari muhallinsu. Yayin da aka samu mummunar ambaliyar ruwa a kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, kana mahaukaciyar guguwa da ake kira Freddy ta haddasa babbar asara a kasashen Malawi da Mozambique.
An ce, sakamakon karuwar zafin yanayi a kai a kai, bala’o’i daban daban za su iya yin mummunan tasiri mafi tsanani a nan gaba.
Sai dai, ban da jure wahalhalun da matsalar sauyawar yanayi ke haifarwa, kasashen Afirka za su iya taka muhimmiyar rawa a kokarin daidaita wannan matsala.
Hakika dimbin albarkatun da nahiyar Afirka ke da su, da matasa masu tarin yawa da al’ummun nahiyar ta kunsa, suna samar da damammaki ga yunkurin sauya salon ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka da na duniya zuwa irin na kare muhalli, da neman raya tattalin arziki ba tare da fitar da iska mai dumama yanayi mai yawa ba.
Kana burin raya tattalin arzikin nahiyar ba tare da haddasa dumamar yanayi ba wani muhimmin batu da ke daukar hankalin mahalarta taron koli na Afirka na tinkarar sauyawar yanayin duniya na farko, da aka kaddamar da shi yau a kasar Kenya.
Ana sa ran ganin gwamnatocin kasashen Afirka za su tsara wata taswirar raya tattalin arziki ba tare da haddasa dumamar yanayi ba a nahiyar Afirka, a wajen taron na wannan karo. Har ila yau, kasashen Afirka za su yi amfani da wannan dama wajen ingiza hadin gwiwar da suke yi tare da abokan hulda na kasashe daban daban, a kokarin tinkarar sauyawar yanayi. Kana hadin gwiwar da suke yi tare da kasar Sin ta riga ta zama wani misali mai kyau a wannan fanni.
Tun daga shekarar 2000, kasashen Afirka da kasar Sin sun jaddada bukatar karfafa hadin giwarsu a fannin kare muhalli, yayin taron ministoci na farko karkashin laimar dandalin hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin (FOCAC). Zuwa yanzu, a karkashin wannan laima, kasar Sin ta riga ta gudanar da wasu ayyuka fiye da dari na samar da makamashi mai tsabta, da samun ci gaban tattalin arziki tare da kare muhalli a lokaci guda, wadanda suka kunshi kafa yankin misali na rage hayaki mai dumama yanayi, da yankin misali na tinkarar sauyawar yanayi a nahiyar Afirka, da taimakawa kasashen Afirka gina “shingen kare kwararowar hamada”, da dai sauransu.
Don neman samun ci gaban tattalin arizki ta wata hanyar da ta dace da ra’ayi na kare muhalli, dole ne a yi kokarin samar da makamashi mai tsabta, wanda ba zai haddasa dumamar yanayi ba. A wannan fanni, hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin ta samarwa nahiyar Afirka da dimbin manyan ayyuka.
A kasar Afirka ta Kudu, tashar samar da wutar lantarki ta karfin iska ta garin De Aar, wadda wani kamfanin Sin ya gina, ta fara samar da wutar lantarki a shekarar 2017, ta yadda aka samu damar saukaka yanayin kunci da kasar ta Afirka ta Kudu ke ciki na karancin wutar lantarki.
Kana a kasar Kenya, tashar samar da makamashi da hasken rana ta Garissa, mafi girma a yankin gabashin Afirka, wadda wani kamfanin kasar Sin ya gina, ita ma ta fara aiki a shekarar 2019.
Inda wutar lantarki da take samarwa za ta iya biyan bukatun iyalai dubu 70, kwatankwacin mutane fiye da dubu 380. Yayin da a kasar Najeriya, tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Zungeru, da wani kamfanin Sin ya gina, tana samar da karin wutar lantarki ta 2.64 billion kWh ga jama’ar kasar a kowace shekara.
Ban da samar da wasu manyan ayyuka, fasahohi na kasar Sin su ma suna taka rawar gani a kokarin raya tattalin arzikin kasashen Afirka gami da magance fitar da iska mai dumama yanayi a lokaci guda.
A watan Maris na bara, kamfanin BasiGo na kasar Kenya ya zama na farko a kasar, a fannin aikin hada manyan motoci na bas masu amfani da wutar lantarki.
Wannan kamfani yana yin amfani da na’urori da kayayyaki da kamfanin BYD na kasar Sin ya samar, wajen hada motocin bas a kasar Kenya. A cewar wani babban darekta na kamfanin, yadda kamfanin na kasar Sin ke raba fasahohi tare da su ya ba kamfanin Basigo damar raya harkoki cikin matukar sauri, ba tare da shan wahalhalu a mataki na farko na sana’ar ba.
Kana a kasar Rwanda, an taba gamuwa da matsalar gina madatsar ruwa kan tushen wani fili mai taushi, yayin da ake gina wata madatsar ruwa kan kogin Nabarronge. Daga baya dimbin cibiyoyin nazarin fasahohi na kasar Sin sun taimaka wajen daidaita wannan matsala, inda suka samar da wata dabara, ta yadda ake iya ci gaba da gudanar da aikin gina madatsar ruwan.
Ta hanyar duba sakamakon da aka samu ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin a fannin raya tattalin arziki ba tare da samun dumamar yanayi ba, za mu iya ganin cewa an lura da hakikanan bukatun da kasashen Afirka ke da su, da kokarin taimaka musu daidaita matsaloli. Kana an samar da sauki sosai ga yunkurin yin hadin gwiwa ta hanyoyi daban daban, da yadda ake mika fasahohi. Zuwa yanzu, hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannin sauya tsarin raya tattalin arziki ta kasashen Afirka zuwa wani nau’i na kare muhalli, da tabbatar da ci gaban kasashen ba tare da samar da iska mai dumama yanayi sosai ba.
A sa’i daya kuma, ana samar da misalai ga sauran kasashe, kan yadda za su iya gudanar da hadin gwiwa tare da kasashen Afirka.
Sa’an nan taron kolin da aka kaddamar da shi a kasar Kenya a wannan karo zai zame wa kasashen Afirka wata kyakkyawar dama ta kara yin hadin kai tare da sauran kasashe, a fannin neman ci gaba ba tare da samar da iska mai dumama yanayi sosai ba. (Bello Wang)