• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wariyar Launin Fata Da Amfani Da Makamai Barkatai Ne Ke Rura Wutar Harbe-Harben Kan Mai Tsautsayi A Amurka

by CMG Hausa
3 years ago
Makamai

A baya bayan nan masharhanta da dama na ta tsokaci game da yawaitar hare-haren bindiga, na kan mai tsautsayi da ake samu a Amurka, lamarin da akasarin masu fashin baki ke alakantawa da mummunar akidar nan ta wariyar launin fata mai tsohon tarihi a kasar, da son cin zali na turawa masu rajin fifita fararen fata, tare da yawaitar mallaka, da amfani da makamai tsakanin fararen hular kasar.

Alkaluma sun nuna cewa, daga farkon shekarar nan ta 2023 zuwa yanzu kadai, an samu harbe-harben kan-mai-uwa da wabi har 146, ciki har da wanda aka hallaka wasu ’yan makarantar firamare 3, da wasu manya 3 a birnin Nashville, da wanda ya auku a jihar Kentucky a ranar Litinin, wanda ya sabbaba rasuwar mutane 4.

  • Xi Jinping: Turbar Zamantarwa Ta Kasar Sin Tana Da Manufa, Tsare-tsare Da Dabaru

A fili take cewa, Amurkawa da shekarun haihuwarsu ya kai 18, na da ikon saye ko rike bindiga, ciki kuwa har da manyan bindigogi masu hadarin gaske, wanda hakan ke kara ta’azzara yanayin tsaron fararen hula. Sannu a hankali, tashe-tashen hankula masu nasaba da harbin bindiga sun samu gindin zama a Amurka. Masana da yawa na cewa, baya ga batun saukin mallakar bindigogi, akwai kuma matsalar fatara, da gallazawa da wasu sassan al’ummun kasar ke fuskanta, wadanda su ma ke kara rura wutar wannan matsala.

Kisan bakar fatan nan mai suna George Floyd, da wasu ’yan sanda fararen fata suka yi a birnin Minneapolis a shekarar 2020, shaida ce da ta kara fayyace yadda wasu sassan al’ummar Amurka ke fuskantar nuna wariya da kyama. Alkaluma sun tabbatar da cewa, mutane da ba asalin fafaren fata ba ne, sun fi fuskantar muzgunawa a Amurka. Kuma wani karin abun takaici ma shi ne yadda wasu ’yan siyasar kasar ke amfani da kalamai na tunzura akidar nuna wariya, a matsayin dabar siyasa ta jan ra’ayin magoya baya.

A daya hannun kuma, mun san cewa cinikin makamai wani ginshiki ne na bunkasar tattalin arzikin Amurka, don haka mamallaka kamfanonin kera makamai, da masu nema musu goyon baya wajen ’yan siyasa, suka zamo kadangaren bakin tulu, wajen dakile matsalar raba fararen hular kasar da makamai masu hadari.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

Abun tambaya a nan shi ne, idan aka gaza kare rayukan al’umma, shin ina sauran wani batun kare hakkin bil adama?

Maimaituwar hare-haren bindiga kan fararen hula a sassan Amurka, na nuni ga yadda gwamnatin kasar ta kasa fahimtar cikakkiyar ma’anar ’yancin bil adama, wanda ya hada da kare rayukan yara kanana, da matasa daga farmakin ’yan bindiga dadi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Next Post
Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 23

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.