Shui Qingxia, mai horar da ‘yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin, tun bayan kama kujerar take daukar nauyi da kalubale na jagorantar kungiyar fita daga mawuyacin hali.
Tana kokari tare da kungiyarta don mika wata takardar amsa ta cimma gasar ta kofin Asiya ga al’ummar kasar baki daya. Da taushin hali da jajircewarta, ta canza makomar kungiyarta, da makomar gungun ’yan mata, har ma da nata makoma.
A shekarar 1983, Shui Qingxia mai shekarun haihuwa 17 a duniya ta samu horo kan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Makarantar Wasannin Matasa ta yankin Hongkou na birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. Ta yi ta haka har tsawon shekaru 6, kuma ta zama zakaran pentathlon na daliban makarantar sakandare ta Shanghai.
A wancan lokacin, tana fatan samun damar haskawa a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, amma an gaya mata cewa saboda tsayin da take da shi, idan ta ci gaba da yin wasan, to ba za ta samu sakamako mafi kyau ba.
Amma, abin farin ciki shi ne, kocin makarantar wasannin yana ganin cewa, Shui Qingxia na da hazaka, kuma abin takaici ne idan aka yi watsi da ita. A daidai wannan lokaci, an kafa kungiyar kwallon kafa ta mata a Shanghai, don haka kocin ya ba da shawarar shigar da Shui Qingxia kungiyar.
Lokacin da ta sami labarin cewa, za ta yi wasan kwallon kafa, Shui Qingxia ta yi mamaki sosai, ta ce, “Me ya sa aka bar ni in buga kwallon kafa? ‘Yan mata suna buga kwallon kafa, yana da ‘ban tsoro’!”
Irin abun da take ji ba abin mamaki ba ne. A wancan lokacin, wasan kwallon kafa na mata ya kasance sabon abu a birnin Shanghai har ma a kasar Sin baki daya, don haka yawancin Sinawa ba su fahimce shi sosai ba.
A wancan lokacin, Shui Qingxia ba ta tsammanin cewa, wasan kwallon kafa, wanda ya sa ta dan jinkirta, zai zama “babban jigo” da ba za ta iya yin kasa a gwiwa ba a rayuwarta ta nan gaba.
A lokacin, tunaninta ya kasance mai sauki kwarai, “Tun da ana son in buga kwallon kafa, to bari in buga.”
Don haka, Shui Qingxia ta fara wasan kwallon kafa a hukumance.
Lokacin da ta fara wasan kwallon kafa, Shui Qingxia ba ta san yadda za ta kare kanta ba, kuma ta kan ji rauni. Ko da yake wasan kwallon kafa yana da wahala, amma Shui Qingxia ta yi mamakin ganin cewa, tana da hazaka a wannan wasan. Tare da hazaka da kuma kokarin da take yi, Shui Qingxia ta yi sauri ta fice daga ’yan matan kungiyar sama da 100, kuma ta shiga tawagar farko ta kungiyar kwallon kafa ta mata ta Shanghai a shekarar 1984. Kana, a shekarar 1986, an zabe ta shiga kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin.
Shui Qingxia ta kasance mai nazarin wasan kwallon kafa a ko da yaushe, a lokacin hutu, ta kan shafe yawacin lokuta wajen kallon wasan, za ta rika lura da motsi, da dabarun ‘yan wasa, da hadin gwiwar dake tsakanin shahararrun ‘yan wasa, da kuma kwarewarsu ta yin nazari wasan a fili, don ganin abin da za ta iya amfani da shi.
Bayan kallon manyan wasannin kwallon kafa na duniya, Shui Qingxia ta fara fahimtar nata kura-kurai, tana bullo da wani tunani, wato samun horo a kasashen waje da sanin al’adun kwallon kafarsu.
A shekarar 1992, Shui Qingxia, wadda ta shafe shekaru 9 tana buga kwallon kafa, ta shiga kungiyar kwallon kafa ta Prema ta kasar Japan, kuma ta kasance daya daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa mata na farko a kasar Sin da suka yi wasa a kasashen waje, tana da shekaru 26 na haihuwa kacal a wannan shekarar.
A kungiyar kwallon kafa ta Prima da ke kasar Japan, Shui Qingxia ta yi saurin zama jigo a kungiyar. Amma a shekara ta biyu da take a kasar Japan, Shui Qingxia ta ji rauni a wasan koyarwa da kungiyar wasan kwallon kafa ta maza, kuma aka saka farantin karfe mai tsayin centimita 30 a cikin kafarta ta dama.
Bayan ta ji raunin, Shui Qingxia ta dawo kasar Sin, kuma bayan watanni 5 kacal, ta bulla a filin atisaye na kungiyar kwallon kafa ta mata ta Shanghai.
Bayan ta murmure daga raunin da ta samu, Shui Qingxia, wadda ta shagaltu da horo da gasa, ba ta da lokacin damuwa da aikin tiyata, hakan wannan farantin karfe ya zauna a kafarta ta dama har tsawon shekaru 7.
A cikin fiye da shekaru goma na buga wasan kwallon kafa, Shui Qingxia ba ta taba tsayawa saboda jin rauni mai tsanani ko maras tsanani ba, muddin tana tafiya a filin wasa, ta kan manta mene ne wahala da gajiya, tana ta guje-guje kamar ba ta jin zafin raunin da take jikinta. Kocin yana damuwa da ita kuma sau da yawa ya yi mata tsawa a wajen filin: “Ki rage gudu kuma ki huta kadan.”
A shekarar 1994, Shui Qingxia ta koma cikin kungiyar kasar Sin, kuma ta halarci gasar wasannin Asiya karo na 12 da aka yi a birnin Hiroshima na kasar Japan a wannan shekarar, inda ta jagoranci kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin wajen lashe lambar zinare.
A cikin gasar cin kofin Asiya guda biyu da suka biyo baya, Shui Qingxia ta taimaka wa kungiyarta lashe gasar. A shekarar 1997, ta kuma lashe gasar cin kofin Asiya karo na biyar a sana’arta.
Ya zuwa yanzu, kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta lashe gasar sau shida a jere tun bayan da ta halarci gasar cin kofin nahiyar Asiya a shekarar 1986, inda ta zama babbar kungiyar kwallon kafa ta mata ta farko a nahiyar. An kuma yi wa Shui Qingxia da abokan wasanta lakabin “‘yan wasan zinare na kasar Sin”.
A shekara ta 2001, Shui Qingxia ‘yar shekaru 35 ta yanke shawarar “rataye takalmanta”. Har ila yau, ba ta da shirin barin wasan kwallon kafa, ta riga ta tsara makomarta: wato za ta zama koci.
Tunaninta na zama koci, ya fara ne tun Shui Qingxia tana matashiya, a shekarar 1999, kafin ta yi ritaya, ta fara halartar darussan zama koci, ta ce, “Tuni na yanke shawara cewa, ina son zama koci, don haka na fara yin shirye-shirye tun da wuri.”
Bayan ta zama koci, ta shafe kusan shekaru 10 a sassan horar da matasa na kasa ko na gida, kuma tana da zurfin fahimtar yadda ake horar da matasa, tsarin bangaren wasan da yanayin al’adu na sana’ar wasan kwallon kafa na mata.
Ta bayyana cewa, “Jagorancin kungiyar matasa da kungiyar yara ya sa na ji cewa, neman ci gaban wasan kwallon kafa na mata na kasar Sin ba abu ne mai sauki ba, ‘yan mata da ke buga wasan kwallon kafa ba su da yawa, kuma iyaye kalilan ne ke son barin ‘ya’yansu su buga wasan kwallon kafa, wanda hakan ke haifar da wahalar zabar kwararru a fannin.”
Matsalolin da Shui Qingxia ta gamu da su a shekaru 10 da suka gabata, su ne har yanzu masu horar da matasa suke fuskanta a shekarar 2022.
A shekarar 2010, Shui Qingxia ta koma birnin Shanghai, inda aka nada ta a matsayin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta matasa mata ta Shanghai, kuma a shekarar 2011, ta jagoranci kungiyar ta lashe gasar kwallon kafa ta mata ‘yan kasa da shekaru 17. Wannan shi ne kofin farko da Shui Qingxia ta lashe a matsayin koci.
A shekarar 2013, ta kai kololuwar aikinta na horarwa a hukumance. A shekarar 2014, ta jagoranci kungiyar lashe gasar kwallon kafa ta mata, kuma a shekarar 2015, ta lashe gasar cin kofin Hukumar Kwallon Kafa ta Sin, da gasar wasan kwallon kafa mata ta Sin wato Women’s Super League, har ma da gasar zakaru ta kasa karo na 13.
A ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, hukumar kwallon kafa ta kasar Sin ta fitar da sanarwar cewa, Shui Qingxia za ta zama babbar kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin. A wancan lokacin, kwanaki 63 kawai suka rage kafin a bude gasar cin kofin nahiyar Asiya.
Shui Qingxia ta ce, “Lokacin da na samu labarin nada ni, gaskiya na san zan fuskanci kalubale, na shafe sama da shekaru 30 a harkar kwallon kafa, kuma tunanin kwallon kafa na mata ya dade a cikin zuciyata, kuma a ko da yaushe ina son zama kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin.”
Har yanzu Shui Qingxia ba ta amince da shan kaye ba, ta ce, “Mutane da yawa na tunanin kafadun mata ba su da karfin daukar kaya, amma ko kungiyar za ta iya cin nasara ko a’a a gasa, wannan ba shi da alaka da jinsin kocin. Na taba rike wannan mukami, kuma na yi nasara, tun da na zabi wannan sana’a, zan zama mai samun nasara, kuma in nuna yadda masu samun nasara suke.”
Har yanzu Shui Qingxia tana iya tuna lokacin da ta fara ganawa da ‘yan kungiyar wasan kwallon kafar mata ta kasar, a lokacin kungiyar tana jimamin kayen da ta sha a wasannin Olympics na Tokyo. Shui Qingxia ta ce, “Babban abin da take ji shi ne kungiyar ba ta yi imani da kanta ba. A gani na, wannan ba shi da kyau, dole ne in gyara tunanin ‘yan wasan ba tare da bata lokaci ba.”
A hirar ta ta farko bayan zama babbar kocin kungiyar kasar, Shui Qingxia ta gabatar da wata kalma, wato “’yan’uwa mata”. Tana fata ’yan kungiyar za su taimakawa juna kamar yadda ‘yan’uwa mata suke yi. Ta ce, “Ba wanda ke farin ciki lokacin da yake cikin koma baya, amma abu mai mahimmanci shi ne yadda za sauya wannan batu. Don haka, tun daga ganawarmu ta farko, na karfafawa kowa da kowa gwiwa, tare da fatan taimakawa dukkan ’yan kungiyar, ta yadda za su dawo da ruhun juriya da sha’awarsu ta samun nasara.”
Ba da dadewa ba, mun ga wannan canji a fagen gasar cin kofin Asiya, kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Sin ta lallasa Taipei ta kasar Sin da ci 4-0, Iran da ci 7-0, sai kuma Vietnam da ci 3-1, kana bayan da suke rashin nasara a baya sau biyu, sun kuma yi kunnen doki sau biyu, kungiyar kwallon kafar mata ta Sin ta kai wasan karshe bayan ta doke Japan a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A karshe dai, tawagar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta sake lashe kofin gasar Asiya bayan shafe shekaru 16, kuma kasar Sin gaba daya ta shiga farin ciki da aka dade ba a manta ba, sanadiyar kwallon kafa.
Shafin yanar gizon Hukumar Kwallon Kafa Ta Asiya wato AFC a takaice ta taba yin sharhi game da Shui Qingxia: Ta fi kowa sanin yadda za a lashe gasar cin kofin Asiya ta mata.
Mutane na cewa, Shui Qingxia ta dawo da ruhi da halayyar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin, kuma ta sauya yanayi da tsarin kungiyar.
A baya jama’a na nuna shakku kan “Ko za ta iya ko ba za ta iya ba”, yanzu mutane suna fatan “Za ta samu nasara yadda ya kamata.” Shui Qingxia ba ta damu da abin da jama’a ke fada ba, abubuwan da take tunani har yanzu, abubuwa masu sauki kamar yadda take wasan kwallon kafa a yayin da take matashiya.
Ta ce, “Ni ma ban sani ba ko zan iya ko ba zan iya ba, abu mafi mahimmanci shi ne, a daina wannan tunanin. Ina burin samun nasara, ina fatan ni da kungiyata za mu dan kara kwazo, ina son kara kaimi wannan karon fiye da baya, ta yadda za mu kai kungiyar ga nasara.” (Bilkisu Xin)