Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ta bukaci al’umma da su hada kai wajen ganin an bunkasa harkokin wasanni a kasar nan.
- Gidauniyar wadda Saraki yake daukar nauyi, ta bayyana haka ne a wajen wasan karshe na gasar kwallon kwando ta Hilltop Pacers Basketball da aka yi a ranar Alhamis.
- Gwamnonin Arewa Na Kokarin Farfado Da Hadin Kan Yankin
- 2023: Duk Da Matsalolin Tattalin Arziki, Bangaren Inshora Da Hannun Jari Sun Bunkasa
“A gidauniyar Abubakar Bukola Saraki muna son wasan kwallon kwando kamar yadda shugaban gidauniyar shi ma yake sha’awa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana .
“Dakta Abubakar Bukola Saraki mutum ne wanda ya yi amanna cewa wasanni suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar rayuwa.
“A kullum maganarsa ita ce yadda za a zajulo matasa masu sha’awar wasan domin samun ci gaba”.
Sanarwar ta kara da cewa “Hakan ne ma yasa jiya, wannan gidauniya ta samu halartar zuwa wajen wasan karshe na wasan kwallon kwando ta Hilltop Pacers Basketball. Kallon wadannan matasan suna jajircewa yana da ban sha’awa sannan yadda ake zura kwallon a cikin kwando shi ma abin burgewa ne da karfafa gwiwa.
Gidauniyar na son ganin ta cike gibin da yake tsakanin wadannan matasan kwallon kwandon, sannan an samar musu da dama da yanayi mai kyau wanda zai sa su nuna bajinta da kwarewarsu tare da cimma burikansu.