Wasu da ake zargin ‘yan daba ne a yammacin Lahadin da ta gabata, sun far wa magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, hari a karamar hukumar Omuma da ke jihar Ribas.
Wata majiya a yankin ta shaida wa LEADERSHIP ce wa, wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP uku ne suke lika fosta na yakin neman zaben Atiku a lokacin da aka kai musu harin ta’addancin.
Babban Jami’in Yakin Neman Zaben Atiku A Abuja, Danladi Zhin, Ya Rasu Yana Da Shekaru 54
2023: Atiku Ya Karyata Batun Zai Goyi Bayan Wike A Zaben 2027
Majiyar ta bayyana daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Nwankwoala Udo, daga kauyen Umuobuo da ke karamar hukumar.
Da yake nanata cewa maharan suma ‘yan jam’iyyar PDP ne daga yankin, ya ce daga baya aka kai mutanen ukun da aka kai was harin asibiti domin kula da lafiyarsu.
Kokarin da aka yi na ganin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP a jihar, Tambari Sydney Gbara, ya mayar da martani kan batun, abin ya ci tura.
Sai dai kuma wani dan jam’iyyar a jihar da ya zanta da LEADERSHIP bisa sharadin sakaya sunansa, ya ce babu yadda za a yi jam’iyyar ta tura ‘yan daba su far wa ‘ya’yanta a jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa rasa samun daidaito tsakanin Atiku da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, tun bayan fitowar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.