1 – Yi wa juna kyakkyawan zato
Yana da muhimmanci ma’aurata su yi wa juna kyakkyawan zato a kowane lokaci. Idan maigida ko uwargida sun ga wani abu da ba su fahimta ba, ya fi kyau su tambaya cikin lumana maimakon su yi zato mara kyau.
- Samun lokacin tare, kuna tattaunawa
Aure ba wai kawai zama tare bane, har da fahimtar juna. Ku ware lokaci don yin magana, musayar ra’ayi, da jin halin da kowa ke ciki. Wannan na karfafa zumunci da kauna.
- Zan Ba Ku $1,000 Kyauta In Zaku Koma Garuruwanku – Trump Ga Baƙin Haure
- Rokar Kasuwanci Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 6 Zuwa Sararin Samaniya
- Yin shawara da juna akan abin da ya shafi rayuwarku
Kowane mutum yana da hakkin yanke shawara, amma a cikin aure, shawara da juna tana kawo fahimta da nutsuwa. Duk wani abu da zai shafi iyali, ku yi shawara tare domin ku yanke hukunci mafi alkhairi.
- Yi wa juna uzuri
Kowa yana da kuskure. Idan daya ya yi laifi, kada a gaggauta fushi ko hukunci. Ku fahimci juna, ku ba da uzuri, sannan ku magance matsalolin cikin lumana.
- Samar da kyakkyawar sadarwa a tsakaninku
Yawan magana da sadarwa mai kyau na hana matsala girma. Idan wani abu ya dame ku, kada ku boye, ku gaya wa juna ta hanya mai dadi da girmamawa.
- Gujewa kwatanta rayuwarku da ta wasu
Kowanne aure yana da nasa halin. Kada ku kwatanta rayuwarku da ta wasu, domin hakan yana iya jefa ku cikin damuwa ko rashin godiya.
- Hana magulmata samun damar shiga tsakaninku
Magulmata da masu kyashi suna iya haddasa matsala a aure. Kada ku bari mutane su rarrashe ku da magana mara amfani ko su haifar da rashin fahimta.
- Bai wa Juna hakkoki
Aure yana da hakkoki. Miji yana da nasa, haka ma mata. Ku rika bai wa juna hakkin da shari’a ta tanada, kamar girmamawa, kulawa, da soyayya.
- Mutunta ra’ayin juna idan bai kauce hanya ba
Kowa yana da ra’ayi da tunani. Idan ba saba wa addini ko al’ada ya yi ba, yana da kyau a girmama ra’ayin juna domin samun zaman lafiya.
- Rashin boyewa juna sirri
Ma’aurata ya kamata su rika yarda da juna. Idan aka fara boye sirri, hakan yana iya kawo rashin yarda da rashin zaman lafiya. Duk wata matsala, ku tattauna tare.
Allah ya sanya albarka cikin zamantakewar aure.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp