Wasu likitoci sun bude kungiyar kula da marasa lafiya kyauta a Abuja, domin taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen samun lafiya.
Kwararriya Nas, Miss Angela Brown wacce ta yi aiki a Kasar Amurka, ita ce ta bayyana hakan lokacin da take ganawa da manema labarai da wata kungiyar mai suna ‘Lan Health Initiatibe’ ta gudanar da taro da ya gudana a ofishin kungiyar da ke Wuse 2 a cikin Abuja.
Ta bayyana cewa Kungiyar Likitoci Masu Zaman Kansu ne makasudin kiran wan-nan taron, domin ‘yan jarida su ne wadanda za su sanar da ‘yan Nijeriya. Ta ce akwai kungiyar mai zaman kanta da take kula da lafiyar ‘yan Nijeriya kyauta ba tare da sun ba da ko kwabo ba.
Ta ci gaba da bayanin cewa ba ita daya ba ce domin kuwa da akwai Dakta Inkechi Mbaezue, sai kuma Dakta Muoneke Lotachukwu wadanda kamar yadda ta kara jaddadawa duk ‘yan Nijeriya ne wadanda a shekarun baya suna zuwa gida Nijeri-ya tun daga Kasar Amerika domin su duba marasa lafiya tare da ba su magani, amma sai suka lura duk wannan ba zai cika masu burin da suke da shi ba, wanda daga karshe suka yanke shawarar dawowa gida Nijeriya. Sai dai kuma ta ce Dakta Muoneke Lotachukwu har yanzu ita tana can Amerika.
Ta ci gaba da bayanin cewa a shekarar 2019, akwai matsalar da ta shafi shaye- shayen miyagan kwayoyi a tsakanin matasa, wanda abin da ya ba su kwarin gwi-wa kenan na tunkabar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), inda suka bayyana musu cewa za su bude wurin kulawa da masu shan miyagun kwayoyi, wanda daga karshe za su iya barin halin shaye- shayen da kuma ma-ganar wayar da kan mutane dangane da illar yin ta’ammuli da miyagun kwayoyi saboda matsalolin da suke tattare shi.
Ta ce da yake da akwai ‘yan Nijeriya masu yawa da suke fama da cututtuka daban- daban sai suka yi shawarar bude ofishi a Nijeriya, domin sun san da akwai mutane wadanda suka fuskanta matsalolin da suka shafi lafiyarsu.
Ta ce akwai hanyoyin da ake bullowa cutar rashin lafiya da ta shafi kwakwalwa da dai sauran cututtuka.