An gurfanar da wasu mutane uku a gaban kotun Majistare ta daya da ke zamanta a Birnin Kebbi bisa zarginsu da cin zarafin babban Alkalin kotun majistare Umar Salihu Kokani ta hanyar lakada masa dukan tsiya.
Mutanen uku da ake tuhumar su ne Aliyu Shehu Jega, Yahaya Badare da kuma Surajo Shehu sannan dukkansu ma’aikatan ne a ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kebbi.
A karar da aka shigar da su mai lamba BK/358c’/2022 akan laifukan hada baki, karya, cin zarafi da bata suna wanda ya saba wa sashi na 373 na kundin Final kod ta jihar Kebbi na shekarar 2021.
Yayin da ya ke gurfanar da wadanda ake tuhumar, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Jibril Abba, ya shaida wa kotun cewa, wadanda ake tuhuma ukun ma’aikatan ma’aikatar ilimi mai zurfi ne ta jihar Kebbi, kuma sun kai wa babban Alkali Kotun majastare Umar Salihu Kokani hari a lokacin da ya ke alwala a masallacin.
Ya shaida wa Kotun cewa, a shirye suke su bude karar nasu, amma saboda rashin halartar babban shaida, za su nemi a dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022 don ci gaba da sauraren karar gadan-gadan.
Hakazalika, wadanda ake tuhumar ba su samu wakilcin wani Lauya a gaban kotun ba
Alkalin kotun, Majistare Hassan Kwaido, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022 domin ci gaba da sauraron karar.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan dage shari’ar, Lauyan majastare Umar Salihu Kokani, Barista Sani Dan-Yaro Majidadi, ya bayyana cewa “Abin da suke so shi ne adalci ga wanda aka ci zarafinsa wanda shi ne Babban Alkalin Kotun majastare ta UKu da ke Birnin Kebbi.”
“Bugu da kari, Barista Majidadi ya yi mamaki, idan wani zai iya kai wa Babban Majistare hari ba tare da wani sakamako ba, zai aika da sigina mara kyau ga jama’a a cikin al’umma cewa za a iya cin zarafin kowa batare da doka ta yi aiki a kansu ko kanta, inji Barista Sani Dan-yaro”.
“Abin da muke so shi ne adalci, ba ma son halin da mutane za su rika daukar doka a hannunsu suna ganin cewa, babu abin da zai faru, a wasu lokutan ma wasu da ake zargin sun kashe wani Majistare a Jihar Kebbi, har ya zuwa yanzu, babu wani abu da aka yi balle mu yi tunanin wani adalci.
“Don haka, muna son lamarin ya canza, don kada mutane su rika daukar doka a hannunsu kuma su kuskura cewa ba za a samu sakamako ba,” in ji shi.