Kwanan baya, Asusun ba da lamuni na IMF ya fidda wani rahoto, wanda ke cewa a halin yanzu, farashin musayar kudi tsakanin kudaden wasu kasashen Afirka da na Amurka na ci gaba da raguwa, lamarin da ya haifar da matsin lamba ga kasashen na Afirka, a fannin ingiza hauhawar fasashin kayayyaki.
Don gane da hakan, wasu kasashen da suka hada da Zimbabwe, da kasar Afirka ta Kudu, sun dauki matakan kara kudin ruwa domin daidaita matsalar hauhawar fasashin kayayyaki a kasashen na su.
Wasu masanan kasashen Afirka na ganin cewa, yadda kasar Amurka ta kara samar da kudade, da kara kudin ruwa, ya lahanta yanayin kasuwannin kasashen duniya.
Game da hakan, tsohon ministan harkokin sadarwa na kasar Zimbabwe Supa Mandiwanzira, ya bayyana cewa, ya kamata a nemi wata hanya ta dakatar da gudanar da cinikayya da kudin Amurka. Ya ce, hakan na nufin a adana darajar kudaden sauran kasashen duniya, domin duk wata kasa mai ’yancin kai, ba za ta cimma nasara ba, idan har tana dogara sosai kan kudin wata kasa ta daban. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)