Daruruwan masu zanga-zanga ne suka mamaye ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza, babban birnin kasar Iraki saboda kone wani Alkur’ani mai tsarki da aka yi a Stockholm, babban birnin kasar Sweden.
Masu zanga-zangar sun zagaye katangar ginin da sanyin safiyar ranar Alhamis tare da cinna mata wuta.
- An Rufe Makarantu A Kenya Saboda Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa
- Babu Sulhu Tsakaninmu Da ‘Yan Fashin Daji -Gwamnatin Zamfara
Zanga-zangar ta zo ne makonni bayan Salwan Momika, dan kasar Iraki mai shekaru 37 da haihuwa, wanda ya tsere zuwa kasar Sweden shekaru da dama, ya kone wasu shafukan littafin Alkur’ani mai tsarki, a daidai lokacin da musulmi suke gudanar da bukukuwan Idin babbar sallah a watan Yuni.
Matakin na Momika ya jawo kakkausar suka daga kasashe da dama, inda Muqtada Sadr, wani malamin Shi’a mai fada a ji a Iraki, ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar adawa da Sweden tare da korar jakadan Sweden.
An gudanar da zanga-zanga guda biyu a wajen ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza bayan kone Alkur’ani, inda masu zanga-zangar suka keta harabar ofishin jakadancin.
A ranar Laraba, ‘yansandan Sweden sun ba da takardar neman “taron jama’a” ga mutane biyu a wajen ofishin jakadancin Iraki a Stockholm a ranar Alhamis.
Ko da yake ‘yansanda ba su bayyana abin da masu zanga-zangar ke shirin yi ba, kafafen yada labaran Sweden sun ruwaito cewa mutanen biyu ciki har da Momika sun shirya kone Alkur’ani da tutar Iraki a wurin taron jama’ar.
Da take mayar da martani akan sabuwar zanga-zangar, ma’aikatar harkokin wajen Sweden ta ce dukkan ma’aikatan ofishin jakadancin Bagadaza suna cikin koshin lafiya, tare da yin Allah wadai da harin.
Har ila yau ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta nuna rashin jin dadi kan harin da aka kai ofishin jakadancin kasar Sweden, inda ta yi alkawarin gurfanar da wadanda suka kai harin a gaban kuliya.