Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana damuwarta ta yadda wasu ‘yan siyasa suke daukar zaben 2023 a matsayin na ko a mutu, ko a yi rai.
Babban jami’an hulda da jama’a na hukumar INEC, Festus Okoye, shi ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a Abuja lokacin kaddamar da tawagar tattauna rikicin zabe, wanda cibiyar bankasa harkokin dimokuradiyya (CDD) ta shirya.
- Ya Kashe Yayansa Kan Kudin Wutar Lantarki Naira 1,500 A Anambra
- Miji Ya Ce Wa Matarsa In Kika Fita Ta Kofa Kin Saku, Sai Ta Fice Ta Taga, Shin Ta Saku?
Ya ce, “Sakamakon yadda ‘yan siyasa suka dauki zaben 2023, na ko a mutu, ko a yi rai kamar dai yaki mai dogon zango,” in ji Okoye.
Ya kara da cewa hukumar INEC tana jin dadin yadda ‘yan jarida suke watsa labaranta, amma ya dace a dunga samun sahihan labarai daga hukumar ta hanyar tuntubarta.
“Hukumar INEC tana da kyakkyawan alaka a tsakaninta da ‘yan jarida wajen bayyana wa al’umma labaranta, amma ana samun labarai karya wanda ake yada wa mutane.
Kamar yadda muke samun karuwar labaran karya da ake jingina wa hukumar, mun dauki matakin yaki da lamarin ta hanyar tsaftace labaran harkokin siyasa musamman ga wadanda suka tsaya takara.”
Ya yaba wa cibiyar CDD bisa kirkiro wannan tsari a lokacin da ya dace domin inganta harkokin hukumar.
Ya ce, “Cibiyar CDD ta nuna cewa ita ba jagoran kungiyoyin farafen huda kadai ba ce, ita mai bunkasa harkokin dimokuradiyyar Nijeriya ce, domin haka muna gode musu kan damuwa wajen abubuwan da suka shafi kasa ta hanyar gudanar da bincike.”
Okoye ya ce ‘yan Nijeriya za su zabe ‘yan takara a mazabe 1,491, ciki har da mazabun ‘yan majalisar dattawa 109 da na wakilai 360 da kuma majalisar dokokin jiha 993 da suke neman kujeru a zaben 2023.
“A kokarinta na shirye-shirye, INEC ta dauki ma’aikata da horar da jami’anta da za a tura su runfunar zabe guda 176,846 da cibiyoyin zabe 8,809 da ke cikin kananan hukumomi guda 774 a fadin jihohi 37 ciki har da Abuja.
“Wannan su suka sa aka kara daukan matakai na tabbatar da an buga tare da bayar da katin zabe ga al’umma kafin babban zaben 2023.
“An gudanar da wannan aikin ne saboda ana tsammanin mutum miliyan 95 za su yi zaben 2023, wanda ya zarce sama da miliyan 20 na yawan kasashe 14 da ke fadin yammacin Afirka.
“Ana tsammanin hukumar ta gudanar da wadannan gagarumin aiki da kyau duk da irin kalubalen da kasar take fuskanta, musamman rashin kyau yanayi na zirga-zirga,” in ji shi.