• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Yankunan Afirka Na Fuskantar Barazanar Yunwa —MDD

by Sadiq
3 years ago
Yankunan Afirka

Yayin da sama da mutane miliyan 41 ke fuskantar tsananin talauci a lokacin rani, musamman a bana, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, matsalar karancin abinci na kara ta’azzara a yammaci da yankin tsakiyar Afirka.

Rahoton bankin duniya ya yi kiyasin, cewa mutane miliyan 29 a halin yanzu sun dogara da taimakon abinci na gaggawa.

  • Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 28
  • Rarara Ya Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Ake Masa

Cibiyar hada-hadar kudin ta duniya, ta dora alhakin yawaitar matsalar karancin abinci mai gina jiki a yankin kan tabarbarewar tashe-tashen hankula, da yawan talauci, da saurin sauyin yanayi, karancin amfanin gona da gurbacewar muhalli.

Gargadin na baya-bayan nan game da karancin abinci ya kuma kara da cewa hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane miliyan 48 a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka rayuwarsu ke cikin hatsari, a kokarin dakile hauhawar farashin kayayyaki da ke haifar da karancin abinci.

Don magance wannan, bankin duniya ya ce ya dauki wani tsari na samar da abinci, musamman mai gina jiki, ta hanyar samar da kudade daga ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa, da kafa bangaren bayar da agajin gaggawa, tattara kudaden ba da agajin gaggawa daga cibiyar Bayar da Tallafi ta Musamman da kuma yin aiki tare da masu aikin jin kai don sa ido kan matsalar rashin abinci.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

Ana sa ran shirin zai lakume dala miliyan 766 a Yammacin Afirka kadai, inda sama da mutane miliyan hudu a fadin yankin za su amfana da shi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, shirin zai yi dukkan mai yiwuwa wajen inganta aikin noma ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
Labarai

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
tinubu
Labarai

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Next Post
An Kwaso ‘Yan Nijeriya 107 Da Suka Makale A Libya

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.