Wata mummunar guguwa ta afkawa gidan kaji na Dauda Mafala da ke Rapomol a karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato a karshen makon da ya gabata, inda ta kashe kaji sama da 3,600.
Lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Ango Da Amarya A Filato
- Sojoji Sun Kwato Haramtattun Muggan Makamai 130 A Jihar Filato
Guguwar ta lalata wasu rumfunan kaji guda shida da wani bangare na katangar gidan kajin da turakun wutar lantarki, da dai sauran gine-gine a gonar.
Manajan Daraktan gonar, Keneth Mafala, ya shaida cewa, an bude gidan gonar tun shekarar 1976, tana cin akalla kaji 60,000.
Mafala ya ce guguwar ta kuma lalata wani kejin kaji mai sarrafa kansa da ya kai zunzurutun kudi har dala 80,000.
“Da misalin karfe 3:30 na ranar Asabar, guguwar iska ta barnata gine-gine da dama a wannan gona.
“Ta lalata wata rumfar kaji da ke da tsuntsaye masu kwai 10,800.
“An yi asarar kaji 3,600, kuma kamar yadda kuke gani, muna ci gaba da kwashe matattun kajin.
“Don haka, adadin na iya karuwa daga lokacin da muka gama.
“Kazalika gaba daya ta lalata wani kejin kaji mai sarrafa kansa da ya kai dala 80,000 da muka shigo da shi a shekarar 2013.
“Wannan injin yana da tsarin tattara kwai, tsarin ciyarwa da kuma tsarin tattara taki,” in ji shi.