Wata kungiya mai zaman kanta ta kaddamar da raba wa ‘yan mata a makarantun Jihar Sakkwato audugar mata kyauta.
Shugaban shirye-shirye na kungiyar, Mista Tayo Fatinikum, ya ce, audugar matan mai suna ‘’Ni Dake Renewable Pad,” an samar ne don a kara bunkasa tsafta a tsakanin ‘yan makaranta da sauran mata a Jihar.
Ya ce, kungiyar ta fahinci bukatar kare mata daga kamuwa da cututtuka da wasu matsalolin da ke tattare da al’adar mata a duk wata.
”Taimakon ya zama dole ne don mata da dama basu da hanyar samun audugar mata a yayin da suke fuskantar al’adar su a duk wata.
”Wasu basa iya zuwa makaranta idan suna a’lada wasu kuma su kan yi amfani ne da tsummokara wajen tare da al’adar.
”Mu muka yi wannan audgar matar ’Ni dake Renewable Pad’ muna kuma karfafa mata wajen yin shi da kansu don yana da saukin hadawa,” in ji Fatinikum.
Ya kara da cewa, wannan shirin suna yi ne da hadin gwiwar hukumar majalisar dinkin duniya ta (UNFPA), don taimaka wajen bunkasa rayuwar mata.
Tunda farko, Kwamishinar mata ta Jihar Sakkwato, Hajia Kulu Sifawa, ta yaba wa kungiyar a kan wannan kokari nata, ta kuma tabbatar musu da hadin kan gwamnati a dukkan harkokinsu, ta kuma shawarci matan da ‘yan matan su shiga yin audugar da kansu, musamman ganin saukin da ke tattare da haka.