Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta damke wata matar aure mai suna Caroline Barka, ‘yar shekara 20, kan zargin kashe mijinta, Barka Dauda, da wuka har lahira.
Caroline Barka mazauniyar Angwan Tamiya ce a karamar hukumar Madagali a jihar.
- Duk Abinda Na Yi A Rayuwata Bazata Ne – Obasanjo
- Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Sun Roki Manyan Kasashen Duniya Su Kawo Musu Dauki
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a jiya Asabar a Yola.
Ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama wacce ake zargin ne a ranar Juma’a, biyo bayan rahoton da aka samu daga wani dan uwan marigayin.
“Fada ne ya barke tsakanin wacce ake zargin, Caroline Barka, ‘yar unguwar Angwan Tamiya, a karamar hukumar Madagali, ita da mijinta mai suna Barka Dauda, bayan da mamacin ya dawo gida a bige, sai ya fada kan jaririnsu dan shekara daya yayin da aka kwantar da shi a kan gado.
“Wannan shaye-shayen nasa, da yawan yin dare da kuma rashin sauke nauyinsa a matsayin miji, shi ne ya fusata wacce ake zargin ta kama marigayin da kokawa har ta kai ga ta daba masa wuka.
“Sakamakon haka ya fadi a sume kuma daga baya aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa,” in ji Mista Nguroje.
Amma ya ce suna gudanar da bincike a kanta kafin su mika ta zuwa kotu.