An ayyana wata sabuwar doka a jihar Mangalmé da ke arewa maso gabashin Kasar Chadi, inda ta nemi matan da suka ki amincewa da tayin auren maza su biya tarar dala 23 zuwa 39.
Wata Kungiyar Addinin Musulunci ce ta Mangalme ta ayyana wannan doka, Sai dai wata Kungiya mai rajin kare hakkin Mata a Chadi ta yi wa dokar tutsu inda ta yi Allah wadai da wannan mataki kuma ta ce wannan kuduri ba ya cikin ka’ida.
BBC Hausa ta rahoto cewa, Kungiyar kare ‘yancin mata ta kasar Chadi ta kaddamar da gangamin neman jan hankali akan shafukan sada zumunta mai taken #stopAmchilini domin nuna kin amincewa da hukunta duk wacce taki amincewa da tayin aure.
Hukuncin kungiyar addinin bata tsaya kan Mata kadai ba, su ma ‘yan Maza in suka ki amincewa da tayin auren mace za su biya tarar dala 15.