Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Muna godiya ga Allah me kowa me komai daya ba mu ikon numfashi, mu ci mu sha mu kwanta mu tashi cikin yardar sa. Kamar kowane mako yau ma filin na tafe da wani batun wanda ya kamata a duba kuma a rika kulawa domin ingantuwar tarbiyya.
A yau zan yi magana ne a kan abin da ya shafi social media wato yanar gizo-gizo, da yawa daga cikin mutane ba su sani ba ko kuma an sani an danne ko ba a nemi sanin ba.
Wayar salula da ake gani ko yanar gizo-gizo tana dab da kai mu wutar jahannama saboda abubuwan da muke yadawa muna kusan fita daga addininmu na musulunci, kusan ma wasu abubuwan mutum yana yin shirka ba tare da ya sani ba.
Na farko muna kusan hada wasu mutane da ubangiji wajen kaunarsu ko wajen yabonsu, wanda kuma Allah baya son kishiya mun riga mun sani.Â
Mutum ka ga a social media yana ta fostin din wani sai ka ga kamar Allah yake kodawa, wannan kirarin za ka ga Allah kadai ne me shi. Za ka ga mutum ya ce “Kai ne komai nawa, ka ne gata na” da dai sauransu to, wannan kuskure ne.
A wani bangaren irin bayanan da muke wani za a ga batsa ce wannan abubuwan sukan yi yaho a kafafen yada labarai ko yanar gizo-gizo, wanda idan wani ya koya ko ya dauka ko ya gani shi ma ya yada to, zunubin mutum yana kanka, ya kamata mu kiyaye.
Duk abin da ka yada idan ka yada alkhairi za ka samu lada, idan ka yada sharri za ka samu sharri. Ita waya da ku ke gani ba wai bature ya yi ta kawai dan ka yada abin da ka ga dama ba.
Na farko ga zumunci sannan zamani ya zo harkar kasuwanci, za ka iya yada abubuwan da ka ke siyarwa, idan fadakarwa ne za ka fadakar, amma dai irin abubuwan da muke yadawa barkatai ‘especially’ ‘yan mata za a ga abubuwan da ake ya wuce misali.
Su kan fitar da tsiraici mace ta dauki hoto ta nuna duk fa wanda ya ga wannan abun to, ba zai iya aurenki ba, ya kamata mu gane babu saurayin da zai ga budurwa a social media tana nuna jikinta/ tsiraicinta ya aure ta babu, ko shi waye magana ta domin Allah, ya kamata a kiyaye musamman mata su suke haka.
Sannan su ma samarin a kiyaye domin su suke tayawa ba dan suna tayawar ba matan ba za su rika sakawa ba, dole ya zamto cewa ana jan hankali wajen a bari a daina ko ba kanwarka bace ba kila ‘yarka ce, ko ba ‘yarka bace ba kila ‘yar’uwarka ce ko ba ‘yar’uwarka ba ce ba kila ‘yar’uwar wani ce, ko ‘yar’uwar abokinka ko kanwar abokinka, irin wadannan abubuwan idan muka hana su za mu ga to, gaba ma ‘ya’yanmu da za su taso ba za su tadda su ba.
Amma idan tun yanzu muke da damar da zamu hana mu tsawatar mu yi wa’azi mu yi nasiha a kai ba a daina ba to, lokacin kuma da babu kai sai ka ga abun ya zo a kan ‘ya’yanka su ma suna yi in ba a lura an fadakar ba.
Dan Allah dan Annabi mu yada abubuwan da zai zamo mana na alkhairi, za mu samu alkhairi idan muka yi na sharri zai zam mana sharri, ko masu yada yabon mutane musamman a bangare na siyasa mu yi hankali mu daina sa mutane a wani bangare wanda za a ga kamar ubangiji ne wannan.
Allah ya sa mu dace .
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp