Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Ribas, Cif Chukwuemeka Woke, ya ce gwamnan Jihar, Nyesom Ezenwo Wike, bai umarci mabiyansa da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 25 ga Fabrairu.
LEADERSHIP ta gano cewar an samu wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa Gwamna Wike ya umarci shugabannin kananan hukumomi da shugabannin jam’iyyar PDP da na mazabu da su zabi Tinubu a ranar Asabar.
- An Ceto Mutane 12 Daga Hatsarin Mota, Wasu Sun Kone Kurmus A Ebonyi
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Oyebanji A Matsayin Gwamnan Ekiti
Amma, da yake magana a wani shirin rediyo da Wakilinmu ya nakalto a Fatakwal a safiyar Laraba, Cif Woke, ya ce masu yada ikirari na zaben Tinubu ba su da gaskiya a bayanan da suka bayyana a ranar jama’a.
Ya fayyace cewa shugabannin sauran jam’iyyun siyasa ne ke zawarcin Wike bisa cancantarsa da ayyukan da ya yi cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Shugaban ma’aikatan gwamnan, ya bayyana cewa har yanzu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, na zawarcin yin sulhu da Wike.
Woke ya ce: “Wike bai taba gaya wa mutanen Ribas cewa su zabi Tinubu ba saboda dacewarsa a siyasance.
Tun da fari dai an bayyana cewar wasu jiga-jigan jam’iyyar APC na zawarcin Wike don komawa jam’iyyar tun bayan da ya fara takun saka da tsagin Atiku.