Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake fitar da wasu bayanai a kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ya ce wasu gwamnonin da suke kusa da Atiku na kitsa masa tuggun ya fadi a zaben 2023.
Wike ya sanar da hakan ne a yayin da ya ke kaddamar da sabin gidajen ‘yan Majalisar Dokoki na jihar.
- Bangar Siyasa Ce Silar Rashin Ci Gaban Arewa –Alhaji Ibrahim
- Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ne, ya kaddamar da aikin.
Gwamnan ya kuma ya kai ruwa rana da Atiku kan yadda Atiku ya dauko gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakinsa ya yi gargadi Atiku kar ya zargi PDP idan har ya fadi a zaben shugaban kasa a 2023.
Ya kuma karyata cewar, ya shigar da karar Atiku da PDP a gaban kotu kan zaben fidda-gwani da PDP ta gudanar a kwanan baya.
Wike ya ci gaba da cewa, “Na yi shiru ne tare da mayar da hankali ne wajen samar wa da romon demokiradiyya ga PDP domin ta lashe zabe amma wasu na ta kokarin kitsa yadda PDP za ta sha kasa a zaben”.
A cewarsa, idan aka fadi a zaben kar wani ya kira sunana kuma na shaida wa dan rakarar hakan amma Atiku, ya tuhumi gwamnonin da ke zagaye da shi, inda ya kara da cewa, suna kitsa yadda za su bata min suna
Wike ya shawarci Atiku da ya umarci sauran mutanen da suke kewaye da shi, da su koma jihohin su domin su tabbatar da cin nasarar PDP a lokacin zaben na Shugaban kasa, inda ya yi nuni da cewa, irin wadandan Gwamnonin ne, suka janyo Atiku ya sha kasa a zaben a 2019.