Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya amince da kashe Naira biliyan 1 a wani mataki na daukar matakan gaggawa don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, musamman a kananan hukumomin Ahoada West da Ogba/Egbema/Ndoni na jihar.
Gwamnan wanda ya jajanta wa wadanda ambaliyar ta shafa, ya kuma kafa wani kwamiti da zai gudanar da aikin raba kayan agajin ga al’ummomin da abin ya shafa a jihar.
Wike, a wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal ta hanyar mai taimaka masa kan yada labarai, Kelvin Ebiri, a ranar Laraba, ya ce an amince da kashe kudaden ne domin baiwa iyalai marasa galihu a kananan hukumomin biyu, wadanda su ne yankunan da lamarin ya fi shafa a jihar, wacce ta mamaye gidaje da filayen noma tare da tilastawa mazauna al’ummomin da abin ya shafa kaura zuwa wasu wurare.
Ya ce, babban sakatare na hukumar ayyuka na musamman (SSB) a ofishin sakataren gwamnatin jihar Ribas, Dokta George Nwaeke, zai yi aiki a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Misis Inime I. Aguma, ita ce Sakatariya.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da, Shugaban karamar hukumar Ahoada ta Yamma, Hon. Fata Ikiriko; Shugaban karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Hon. Vincent Ayuba; Hon. Onowu Emeka Anyasodike da Daraktan gudanarwa a ma’aikatar ayyuka na musamman.
Dukkan mambobin kwamitin zasu hallara a gidan gwamnatin dake Fatakwal a ranar Alhamis.