Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a daren Lahadi ya tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, a Birnin Fatakwal, babban birnin jihar, gabanin kaddamar da titin Mgbutanwo da ke karamar hukumar Emohua a yau Litinin.
Wike ya gayyaci ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa bude ayyukansa daban-daban a Ribas, ya ce ya gayyaci ‘yan siyasa daga Jam’iyyun adawa don bude ayyuka a jiharsa domin su gani da idonsu su kuma shaida wa ’yan jam’iyyunsu.
- 2023: Wike Zai Goyi Bayan Peter Obi Ya Yi Watsi Da Takarar Atiku
- Rikicin PDP: Ina Farin Ciki Da Sulhun Da Rundunar Wike Ta Nemi A Yi – Atiku
Tsohon shugaban jam’iyyar (APC) na kasa, Adams Oshiomhole a ranar Larabar da ta gabata ya kaddamar da gadar sama ta 8 a jihar da ke kan titin Ada George, cikin karamar hukumar Obio-Akpor.
Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kaddamar da gadar sama ta 9 a babbar mahadar Ikoku a ranar Alhamis.
Hakazalika, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da makarantar koyon aikin lauya ta Nijeriya a Fatakwal ranar Juma’a.
Kusan kimanin watanni, Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP da aka fi sani da ‘Yan G5 suna neman shugaban Jam’iyyar, Iyorchia Ayu da ya yi murabus, suna masu cewa bai kamata ‘yan Arewa su zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa ba kuma dan takarar shugaban kasa ya fito daga yankin ba.
Sai dai kuma, Ayu, dan asalin jihar Benue, ya dage kan cewa ba zai sauka ba har sai karshen wa’adinsa na shekaru hudu sun cika, ‘Yan G5 din sun gindaya sharadin sai ya yi murabus a matsayin wani sharadi na goyon bayan Atiku Abubakar, a zaben 2023.
Yayin da ba a ganin Wike da abokansa suna yi wa Atiku kamfen ba, ba a san ko za su goyi bayan Bola Tinubu na jam’iyyar APC ko Obi ba a takarar neman kujerar fadar Aso Rock wanda manazarta da masu lura da al’amura suka bayyana a matsayin tseren doki uku.