Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, ta yi barazanar kwace filaye 9,671 ga wadanda ba su biya harajin filaye na shekarar 2023 a cikin makwanni biyu masu zuwa ba.
Wadanda ke sahun gaba da ba su biya harajin ba sun hada da; ofisoshin jakadancin kasashen waje, wadanda ake bin su kimanin dala miliyan 5.3.
- Da Ɗumi-ɗumi: Bayan CBN, FAAN, Manyan Ma’aikatun Hukumar Man Fetur Na Shirin Komawa Legas
- Jirgi Mai Saukar Ungulu Kirar Kasar Sin Ya Kammala Gwajin Tashi Da Sauka A Yanayin Hunturu
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, sai kuma kamfanoni da sauran daidaikun mutanen da ake bin su kudin harajin kimanin Naira 2,205,079,937.
Har ila yau, Hukumar Babban Birnin Tarayyar, a cikin kunshin sanarwar ta kara da cewa, ta na kara tunatar da wadanda suka mallaki wurare a Abujan; wajen ci gaba da biyan harajin da doka ta tanadar a kan duk wanda ya mallaki fili, sannan za a iya biyan wannan haraji tun kafin lokacin biyan ma ya yi.
Haka zalika, Ministan Abuja Nyesom Wike, ya nemi shugabanni da sauran wadanda suka mallaki wurare daban-daban a fadin babban birnin tarayyar, da su gaggauta biyan harajin da dokar ta tilasta musu biya, domin aiwatar da ayyukan raya kasa a ciki da sauran kewayen na Abuja.
Ministan ya yi wannan kira ne, a lokacin gudanar da duba ayyukan da ake aiwatarwa; ciki har da gidan Mataimakin Shugaban Kasa, wanda a halin yanzu Kamfanin Julius Berger ke kan ginawa a Asokoro da kuma aikin shataletalen da ake kan yi a ‘Area 1’, wanda Kamfanin CGC ke ginawa duk dai a babban birnin tarayyar.
Sannan akwai aikin gada na Wuye, wanda shi ma a halin yanzu ake kan aikinsa ka’in da na’in karkashin Kamfanin Arab da kuma titin D6 da B12, wanda shi ma Kamfanin Julius Berger ne ke aiwatar da shi.