Cibiyar Binciken Ƙwaƙwaf a Kafafen Yaɗa Labarai ta Wole Soyinka (WSCIJ), ta gayyaci Farfesa Umaru Pate, Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere, domin ya kasance cikin kwamitin amintattunta.
Wannan gayyata, wacce Daraktar Gudanarwar cibiyar, Motunrayo Alaka, ta aikewa Farfesa Pate, ta nuna girmamawa ga rawar da yake takawa a fagen aikin jarida a Nijeriya da duniya baki ɗaya, da kuma bunƙasa binciken ƙwaƙwaf a kafafen yaɗa labarai.
- Dakatar Da Gwamna Fubara: Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hafsan Sojin Ruwa A Matsayin Mai Kula Da Jihar Ribas
- Atiku Ya Soki Tinubu Kan Ayyana Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas
A cikin wasiƙar, Alaka ta jinjina irin gudunmawar da Farfesa Pate, ke bayarwa a matsayin ƙwararre a fannin aikin jarida da ci gaban al’umma da kare haƙƙoƙin ɗanadam, inda ta jaddada jajircewarsa wajen haɓɓaka fannin yaɗa labarai da ci gaban al’umma a faɗin duniya.
Da wannan sabon matsayi, Farfesa Pate, zai haɗa kai da sauran ƙwararru da ke aiki domin tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da inganta shigar da al’umma cikin harkokin shugabanci, wanda ake kyautata zaton ƙwarewarsa za ta taimaka wajen tsara sabbin hanyoyi da cibiyar WSCIJ za ta amfana.
WSCIJ, wacce an sanya mata suna daga fitaccen marubuci kuma masanin adabi, Farfesa Wole Soyinka, cibiya ce mai zaman kanta da ke amfani da binciken ƙwaƙwaf a aikin jarida domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta tsarin shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp