A kalla ‘yan Nijeriya mutum 112 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hadurran da suke da alaka da wutar lantarki a shekarar 2024, kamar yadda rahoton zango da hukumar kula da wurin wutar lantarki a Nijeriya (NERC) ta fitar.
Rahoton ya kuma nuna cewa wadannan adadin mutuwar ya faru ne a cikin hadurra guda 228 da aka samu wanda ya jikkata wasu karin mutum 108.
- Gobara Ta Ƙone Shaguna 3 Da Kayayyaki Masu Yawan Gaske A Ibadan
- Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Jerin mace-macen sun kunshi cewa mutum 23 da suka mutu sakamakon hadurra 55 da suka faru a farkon zangon shekarar 2024, inda wasu 31 kuma suka jikkata. A zango na biyu kuma an samu rahotonnin hatsarin wutar lantarki guda 63, inda a cikin wannan aka samu matattu 34 da wasu 17 da suka raunata.
Sai kuma a zango na uku da aka samu hatsarin wutar lantarki guda 56 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 29 da jikkata wasu 38, sai kuma a zango na karshe aka samu faruwar hatsarin sau 54 da ya janyo asarar rayuka 23 da jikkata wasu 19.
Rahoton ya nuna cewa mutum 33 sun rasa rayukansu ne sakamakon hadewar wayoyin lantarki, yayin da wannan matsalar ta jikkata wasu 13.
Haka zalika, mutuwar mutane 33 da jikkata 54 sun faru ne sakamakon munanan ayyuka na ganganci da rashin yanayi mai kyau, yayin da yin aiki ba bisa ka’ida ba ya kai ga mutuwar 23 da jikkata shida.
Masu barnatawa da lalata kayan wuta sun janyo mutuwar mutane 18 da jikkata wasu 7, sai kuma hatsarin fadowa daga sama ya janyo mutuwar mutum daya da jikkata wasu 18.
A Nijeriya dai sama da shekaru ana fama da matsalar rasa rayukansu da jikkata mutane da dama daga hadurran da suka shafi na wutar lantarki kuma wannan mafi akasari na faruwa ne sakamakon amfani da kayan wuta marasa inganci ko marasa kyau, karancin amfani da kayayyakin kariya, ayyukan masu lalata kayan wuta da kuma yin gina kusa ko a kasar layukan wutar lantarki da dai sauran matsalolin.
Da yake zantawa da manema labarai, Manajan Daraktan Hukumar Kula da Ayyukan Wutar Lantarki ta Nijeriya (NEMSA), Injiniya Aliyu Tahir, ya ce binciken da aka yi a kan dukkan hadurrukan da suka wakana ya zuwa yanzu ya nuna cewa da yawa daga cikinsu wadanda lamarin ya shafa sun hada da ma’aikatan kamfanonin samar da wutar lantarki.
Injiniya Tahir ya lura kan cewa hadurran mafi yawansu sun faru ne sakamakon rashin kin bin ka’idojin aiki da matakan kariya a yayin gudanar da aiki da aikin kula da lamuran wuta.
“Muna ganin yadda ma’aikata ke aiki kan layukan wutar lantarki ba tare da kayan aikin kariya na ma’aikata ba.
“Muna kuma ganin yadda wasu ke hanzari da gaggawa yayin aikin gyara wuta. Wannan fa wutar lantarki ne. Wutar lantarki na tattare da abubuwa masu hatsari sosai, wadannan hatsarin suna kuma shafan masu gudanar da aikin, don haka bin matakan kariya da kiyayewa da sanya kwarewa a bangaren aiki ne kawai zai kai ga rage matsalolin nan,” ya shaida.
Ya ce, hukumar tana kan sake nazarta matakan kariya domin tabbatar da kamfanonin wutar lantarki suna bi domin kare kai tare da sahalewa da amincewar NERC.
Alkalin-alkalan Nijeriya, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta yi kira ga bangaren shari’a da su tabbatar da daukar nauyin kamfanonin wutar lantarki da aka samu sakamakon mace-macen wutar lantarki a kasar nan.
Da take jawabi yayin wani taron kara wa juna sani da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta shirya a Abuja, ta bayyana fargaba kan mutuwar mutane 112 da suka samu wutar lantarki da kuma jikkata 95 a shekarar 2024 kadai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp