Shugaba Xi jinping na kasar Sin ya halarci taron mataki na biyu, na kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 32, da ake gudanarwa a Gyeongju na kasar Koriya ta Kudu, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi.
A cewar shugaba Xi, duniya na fuskantar sabon zagayen gagarumin sauyi a fannonin kimiya da fasaha, gami da masana’antu, inda wasu sabbin fasahohi, ciki har da kirkirarriyar basira ta AI, suka nuna alkiblar da al’ummar dan Adam za ta dosa. Sai dai a sa’i daya kuma, karuwar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya, yayin da ake fuskantar karin matsaloli a fannonin sauyawar yanayi, da samar da abinci, da makamashi, da dai sauransu.
Shugaban ya bukaci kasashe daban daban dake yankin Asiya da na tekun Pasifik, da su karfafa hadin gwiwa, a kokarin tabbatar da wata kyakkyawar makoma, inda ya ba da shawarwari guda 3, wato: Ta farko, a yi amfani da sabbin fasahohi wajen raya tattalin arziki. Ta biyu, tsayawa kan matakan kare muhalli, don tabbatar da ci gaba mai dorewa. Kana shawara ta uku ita ce, yayata dabaru masu inganci don ganin ci gaban tattalin arziki ya amfani kowa.
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)














