Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, sun aike da wasikar taya murna ga taron tattaunawa karo na 10 na jam’iyyun siyasa masu mulkin Sin da Rasha.
Cikin wasikarsa, Xi Jinping ya ce, dangantakar Sin da Rasha ta jure tarin kalubaloli daga sauye-sauyen yanayin duniya, inda ta ci gaba da ingantuwa da zama sabon abun koyi a tsarin dangantakar manyan kasashe, wadda ke da muhimmanci gaya ga tabbatar da ci gaba da ma zaman lafiya a duniya. Ya ce tsarin tattaunawa tsakanin jam’iyyu masu mulkin Sin da Rasha, ya zama wata sabuwar hanya da kuma dandali da kasashen biyu za su karfafa aminci da juna a bangaren siyasa da hada hannu da inganta hadin gwiwar moriyar juna.
A tasa wasikar taya murnar, Vladimir Putin ya ce, kasashen biyu na aiki tare domin daukaka wasu manyan ayyukan hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da sufuri da makamashi da al’adu da sauran wasu fannoni, kuma suna hadin kai ta hanyar tsare-tsaren hadin gwiwa a tsakaninsu da ma wanda ya hada da kasa da kasa kamar kungiyar hadin kai ta Shanghai da BRICS, da zummar warware manyan batutuwan dake ci wa duniya tuwo a kwarya da gina tsarin tafiyar da harkokin duniya mai cike da adalci bisa turbar demokradiyya. (Fa’iza Mustapha)