Kungiyar Dalibai ta Jami’ar Koyarwa ta Modibbo Adama da ke Yola (SUG), ta yaba da biyan kudin makaranta ga dalibai 308 da Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya, Sanata Aminu Iya Abbas, ya yi.
Shugaban kungiyar, Kyauta Samuel Tari, ya bayyana haka a Yola, ya ce “biyan kudin makaranta ga dalibai a wannan mayuwacin halin da muke ciki, babban karfafa gwiwa ne ga matashi.
“Tallafa wa harkar ilimi, kamar kawar da halin lalacewa a tsakanin matasa ne, zai kuma mayar da daliban wannan yanki hanya su ci gaba da karatu ba tare da matsala ba” in ji Kyauta.
A cikin wata sanarwar manema labarai da mai taimaka wa Sanatan kan harkokin kafafen sadarwa, Muhammad Ahmad, ya ce Sanata Iya Abbas, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kimiyya da fasaha da sabuwar al’ada, ya biya kudin makaranta ga dalibai 308.
Sanarwar ta ce Sanatan ya dauki matakin ne biyu bayan halin kunci, fatara da wahalhalun da ya hana daliban su biya kudin, ya ce biyan kudin na nuni yaran talakawa za su samu damar samun ingantaccen ilimi.
Sanarwar ta kuma bada bayanin kowace karamar hukuma da daliban da aka biyawa.
Karamar Hukumar Fufore dalibai 14, Yola ta Arewa 87, Yola ta Kudu 61, Girei 36, Song 25, Hong 59 da kuma Karamar Hukumar Gombi 26.