Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa.
Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan sabon tafarki, ana fatan Jam’iyyar Zhigong ta ci gaba da zaune bisa jagorancin JKS, ta kuma kara zurfafa fahimta da aiwatar da tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, ta hada kai da ’yan uwa Sinawa dake ketare, da wadanda suka dawo gida, da kuma daliban dake karatu a kasashen waje, don ba da gudunmawa ga babban aikin dunkulewar kasar, da kuma taka rawar gani ga aikin gina kasa mai karfi ta hanyar zamanintar da al’umma da kuma farfado da al’umma.
An gudanar da babban bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin a yau Juma’a 19 ga wata a nan birnin Beijing. shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na Sin Wang Hu’ning ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp