Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da hada karfin dukkan mutanen dake da aikin yi, wadanda ke aiki tukuru bisa kankan da kai, domin ganin tabbatuwar burin farfado da kasar Sin a zahiri.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar gamayyar kungiyoyin kwadago ta kasar da karrama ma’aikata abun koyi da ma wadanda suka kasance abun misali.
An karrama jimillar mutane 1,670 a matsayin ma’aikata abin koyi na kasa, yayin da mutane 756 aka karrama su a matsayin abin misali. Baya ga wadanda ke aiki a sassa na yau da kullum kamar aikin gona da masana’antu, daga cikin wadanda aka karrama akwai magada kyawawan al’adun gargajiya na kasar Sin da wakilai daga sabbin sana’o’i kamar su ma’aikata masu isar da sakonni, da masu horar da masu ba da hidima a gidaje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp