Yau Alhamis, an bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, inda ya gabatar da jawabi mai taken “Mu hada kai domin inganta harkokin zamanantarwa, da kuma gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya”.
Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, kafuwar dandalin FOCAC a shekarar 2000 yana da muhimmanci matuka wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. Cikin shekaru 24 da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afirka sun fahimci juna da goyawa juna baya, lamarin da ya kasance abin koyi wajen kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa.
Xi ya sanar da cewa, za a daga huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wadanda suka kulla huldar diflomasiyya da Sin zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da kuma mai da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a matsayin dangantakar gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a dukkan fannoni cikin sabon zamani.
Xi ya ce, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su hada kansu domin inganta harkokin neman zamanantarwa a fannoni guda shida, wato neman zamanantarwa cikin yanayin adalci, da neman zamanantarwa mai bude kofa ga waje da cimma moriyar juna, da neman zamanantarwa mai bautawa jama’a, da neman zamanantarwa mai nuna fahimtar juna, da neman zamanantarwa ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma neman zamanantarwa ta hanyoyin zaman lafiya da tsaro.
Ya kuma kara da cewa, cikin shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen Afirka wajen tsara manyan matakan sada zumunci da neman zamanantarwa a fannoni 10, domin zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka, tare da ba da jagoranci ga kasashe masu tasowa kan harkokin zamanantar da kasashen. Wadannan manyan matakai sun kuma hada da fannonin musayar al’adu, da karuwar cinikayya, da hadin gwiwar tsarin samar da kayayyaki, da bunkasa harkokin sadarwa, da raya hadin gwiwa, da inganta harkokin kiwon lafiya, da raya aikin gona da tallafawa al’umma, da karfafa mu’amala a tsakanin jama’a, da neman bunkasuwa ta hanyar kare muhalli, da kuma inganta ayyukan kiyaye tsaro.
Bugu da kari, ya ce, ba za a bar kowa a baya ba kan hanyar neman zamanantarwa. Bari mu hada kan al’ummomin Sin da Afirka biliyan 2 da miliyan dari 8, domin inganta zamanantarwar dukkanin kasashe maso tasowa ta hanyar zamanantar da Sin da Afirka, gami da samar wa kasashen duniya wata makoma mai haske, wadda take da zaman lafiya da tsaro, da wadata da kuma ci gaba. (Mai Fassara: Maryam Yang)