A yau Asabar 12 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da rubutaccen jawabi, ga dandalin tattaunawar kasa da kasa kan “Taimakawa kasashen waje a fannin noman shinkafa mai aure, da kuma samar da isasshen abinci na duniya”.
A yayin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, samar da isasshen abinci, muhimmin batu ne da ya shafi rayuwar bil’adama. Ya ce kimanin rabin karni da ya gabata, an samu nasarar yin nazari, da samar da shinkafa mai aure tare da yayata fasahar a kasar Sin, wanda hakan ya taimaka wa kasar Sin wajen amfani da kasa da kashi 9% na filayen noma a duniya, don warware matsalar abinci ga kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, kuma ta zama kasa mafi girma wajen noman hatsi a duniya, kuma kasa ta uku wajen fitar da hatsi.
Tun daga shekarar 1979, shinkafa mai aure ta bazu, zuwa kusan kasashe 70 dake nahiyoyin duniya biyar, inda ta ba da gudummawa sosai wajen habaka noman hatsi, da raya aikin gona a kasashe daban-daban, da samar da irin wannan hanya da ta dauka ta warware matsalar karancin abinci ga kasashe masu tasowa.
Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashe daban daban, wajen karfafa hadin gwiwa a fannin samar da abinci da rage radadin talauci, da ba da gudummawa sosai wajen gaggauta aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa na MDD kafin shekarar 2030, da gina duniyar da za ta kubuta daga yunwa da talauci. (Mai fassara: Bilkisu Xin)