• English
  • Business News
Tuesday, September 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin Kungiyar APEC Karo Na 29

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin Kungiyar APEC Karo Na 29
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 29 a yau Juma’a.

Xi ya bayyana cewa, ya kamata a tabbatar da adalci a duniya, da gina yankin Asiya-Pacific mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, kana ya yi kira ga bangarori daban daban su gina makoma ta bai daya ta Asiya-Pacific tare, da kuma samun sabuwar nasara a kan hadin gwiwar yankin.

  • Sin Na Ba Da Gudunmawar Ci Gaban Duniya

Xi Jinping ya jadadda cewa, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan bude kofa da gina Asiya-Pacific inda jama’a za su sami wadata tare. Ya ce a shekarar badi, bangaren Sin zai yi tunanin gudanar da dandalin tattaunawar koli na hadin gwiwar duniya kan shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za a samar da sabon kuzari ga neman ci gaba da samun nasarori a yankin Asiya-Pacific da ma duniya baki daya.

Xi Jinping ya ce, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan samu ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli, da gina Asiya-Pacific mai tsabta da kyan gani. Yana mai cewa, bangaren Sin zai bayar da goyon baya don cimma makasudin Bangkok, tare da maraba da kasashen Asiya-Pacific su shiga cikin ajandar ci gaban kasa da kasa.

Har ila yau, Xi Jinping ya bayyana cewa, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan samar da makoma ta bai daya, da gina yankin Asiya-Pacific ta yadda za a rika taimakawa juna. Kuma ya kamata a dage wajen kiyaye manufofin kungiyar APEC, da karfafa huldar abokantaka ta aminci da hakuri da juna da hadin gwiwa da samun nasara tare.

Labarai Masu Nasaba

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

Bugu da kari, ya ce, Sin za ta dade tare da kara bude kofarta ga kasashen waje cikin fage mai fadi da zurfi, da nacewa bin hanyar zamanintarwa iri na kasar Sin, da gina babban sabon tsarin tattalin arziki mai bude kofa, da samar da ci gaba da yayata gogewarta na ci gaba ga duniya musamman ma Asiya-Pacific.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Fashin Baki A Kan Fina-finai Da Rubuce-rubucen Batsa

Next Post

Sake Kunno Kan Siyasar Kabilanci

Related

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
Daga Birnin Sin

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

40 minutes ago
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Daga Birnin Sin

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

2 hours ago
Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

21 hours ago
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
Daga Birnin Sin

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

22 hours ago
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Daga Birnin Sin

Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”

23 hours ago
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

24 hours ago
Next Post
Sake Kunno Kan Siyasar Kabilanci

Sake Kunno Kan Siyasar Kabilanci

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

September 16, 2025
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

September 16, 2025
Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

September 16, 2025
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

September 16, 2025
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

September 16, 2025
Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci

Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci

September 16, 2025
DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu

DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu

September 16, 2025
Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi

Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo

September 16, 2025
Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?

Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?

September 16, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.