Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban gidauniyar Bill & Melinda Gates na kasar Amurka wato Mista Bill Gates a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A yayin ganawarsu, Xi Jinping ya nuna yabo matuka game da kokarin da Bill Gates da gidauniyarsa suka yi wajen inganta aikin kawar da talauci, da kiwon lafiya, da neman ci gaba, da kuma aikin jin kai a kasashen duniya.
Xi ya jaddada cewa, kasar Sin na dukufa wajen neman farfadowar kasa baki daya ta hanyar zamanintarwa, za ta kuma yi hadin gwiwa da kasashen duniya domin samun bunkasuwa tare, ta yadda za a karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama.
Kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da gidauniyar Bill & Melinda Gates, da kuma samar da taimako da goyon baya ga kasashe masu tasowa.
A nasa bangare kuma, Bill Gates ya ce, kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin kawar da talauci da yaki da annobar COVID-19, lamarin da ya kasance abin koyi ga kasashen duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)